Zamfara: Mun dauki masu gadin al’umma 4200 don yaki da ‘yan ta'adda

Zamfara: Mun dauki masu gadin al’umma 4200 don yaki da ‘yan ta'adda

  • Gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da daukar maaikatan gadin rayuka da kadarorin al'umma 4200 don yaki da ta'addanci
  • Kwamishinon Ibrahim Dosara da Mamman Tsafe sukasanar da hakan ga manema labarai a garin Gusau
  • Sun bayyana yadda zaman lafiya ke dawowa jihar a hankali dub da yadda ake taruka ba tare da fargaba a yanzu

Zamfara - Gwamnatin Zamfara ta ce ta dauki jami’an kare al’umma 4,200 aiki a wani mataki na dakile ayyukan ‘yan bindiga a jihar, The Cable ta ruwaito.

Ibrahim Dosara, kwamishinan yada labarai da Mamman Ibrahim Tsafe, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida ne suka bayyana hakan a wata zantawa da manema labarai a ranar Lahadi.

Zamfara: Mun dauki masu gadin al’umma 4200 don yaki da ‘yan ta'adda
Zamfara: Mun dauki masu gadin al’umma 4200 don yaki da ‘yan ta'adda. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Kwamishinonin sun ce sannu a hankali zaman lafiya yana dawowa jihar duk da "ayyukan 'yan kasuwa marasa kishin kasa".

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga suka hallaka 'yan sanda da dama a Kebbi

Sun ce masu gadin al'umma 4,200 sun hada da tsoffin ma'aikata, masu aikin sa kai, da sauran mazauna wurin, TheCable ta ruwaito.

Kwamishinonin sun ce, CPGs za su tallafa wa jami’an tsaron jihar domin tunkarar ‘yan bindigar a yankunansu.

Sun bada tabbacin cewa nan bada jimawa ba Zamfara ta dawo da martabar ta ta baya a matsayin daya daga cikin jihohin Najeriya masu zaman lafiya.

“Yan Najeriya da dama ba su sani ba, ban da ‘yan bindiga, akwai wasu ‘yan siyasa marasa kishin kasa, masu rigingimun siyasa da ke da niyyar yi wa shirin zaman lafiya zagon kasa saboda son zuciya ko dai su samu mulki ko kuma su dakile nasarorin da gwamna zai samu ga jihar Zamfara da ‘yan kasa,” inji su. yace.

Kara karanta wannan

2023: Bayan Uba Sani, Kwamishina a Kaduna Ya Ce Shima Yana Son Ya Gaji El-Rufai

“Muna sanar da cewa, Insha Allahu nan ba da jimawa ba jihar Zamfara za ta dawo da martabar ta ta baya a matsayin daya daga cikin jihohin da suka fi zaman lafiya a tarayyar Najeriya.
“Zai iya ba ku sha’awa idan kuka lura da cewa an samu zaman lafiya a kusan dukkan sassan arewacin jihar, inda wasu ‘yan ta’adda suka yi ta fama nan da can. Ina da yakinin cewa samun nasara kashi 100 ba za ta taba zama al'amarin kwana daya ba.
“Domin dakile wannan ikirari, a kwanakin baya ne gwamnatin jihar Zamfara ta karbi bakuncin dimbin jama’a a Gusau, babban birnin jihar, daga ciki da wajen jihar. Wadanda suka zo Gusau suka zauna har tsawon mako guda ba tare da an yi musu fashi da makami ba,"yace.

'Yan ta'adda sun sace mutum 75 a samamen da suka kai kauyukan Zamfara

A wani labari na daban, 'yan ta'adda da ake zargin 'yan bindiga ne sun sace a kalla mutum 75 a yankin Kekun Waje ta karamar hukumar Bungudu a jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Jigawa: Hukumar Hisbah ta kama maza da mata 61 da ake zargi da aikata masha'a

A wani samame da miyagun suka kai sama da wata daya da ya gabata, sun yi garkuwa da sama da mutum 60.

Wadanda aka sace a wancan lokacin har yanzu suna hannun miyagun, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel