Da Dumi-Dumi: Gwamna Buni ya yi amai ya lashe, ya amince da abubuwan da Bello ya zartar

Da Dumi-Dumi: Gwamna Buni ya yi amai ya lashe, ya amince da abubuwan da Bello ya zartar

  • Shugaban kwamitin rikon kwarya na APC ta ƙasa, Mala Buni, ya ce ayyukan da Bello ya yi da baya nan suna kan doka kuma sun zartu
  • A cewar Buni kafin tafiyarsa Dubai duba lafiya, ya rubuta takardan miƙa ragamar jagorancin APC ga gwamnan Neja, Abubakar Bello
  • Sai dai bai bayyana matakin tsige Sakataren APC na ƙasa da Bello ya yi ba yayin da baya nan

Abuja - Shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC ta ƙasa, Gwamna Mala Buni na Yobe, ya yi fatali da raɗe-raɗin warware duk ayyukan da shugaban riko, gwamna Bello ya aiwatar.

Vangauard ta rahoto cewa Buni ya musanta soke kananan kwamitoci da gwamna Neja, Abubakar Bello, ya kafa lokacin da yake Dubai, ya amince da ayyukan baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Labarin cikin Hotuna: Mai Mala Buni yayi takakkiya zuwa Landan don ganin Shugaba Buhari

Sai dai har yanzun babu cikakken bayani ko amincewar da Buni ya yi wa ayyukan Bello, har da tsige sakataren CECPC, Sanata John James Akpanudoedehe.

Gwamna Mala Buni na Yobe
Da Dumi-Dumi: Gwamna Buni ya yi amai ya lashe, ya amince da abubuwan da Bello ya zartar Hoto: Hon Mai Mala Buni/facebook
Asali: Facebook

Wannan matakin ba ya rasa nasaba da dabarun bangaren Buni na sansatawa da mambobin CECPC da ke ganin an musu ba dai-dai ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A ranar Alhamis da ta shuɗe, Buni ya rushe dukkan jerin kananan kwamitoci da gwamnan Neja ya kafa domin taimaka wa wajen shirya babban taro na ƙasa.

A wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Sakataren APC na ƙasa, Buni ya zare sunayen mambobin CECPC daga Kwamitocin inda ya bar kansa da sakatare kaɗai.

Sai dai hakan bai yi wa bangaren gwamna Bello daɗi ba, nan take suka fitar da bayanin cewa sun amince da tsige Sanata James Akpanudoedehe daga matsayin Sakatare.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta bayyana yan majalisu 14 da zata baiwa tikitin takara kai tsaye a 2023

A wata sanarwa da ya sawa hannu da kansa, Buni ya ce ya miƙa ragamar jagoranci hannun gwamna Bello kafin tafiyarsa, dan haka duk matakan da ya ɗauka suna kan doka.

Punch ta rahoto Mala Buni ya ce:

"Muna mai sanar wa masu ruwa da tsaki da mambobin jam'iyyar cewa zancen soke duk ayyukan da shugaban riko, gwamna Bello na jihar Neja ba gaskiya bane."
"Saboda haka, duk ayyukan da aka aiwatar lokacin da bana ƙasa suna nan daram kuma a kan doka. Muna shawartan masu faɗa aji da mambobin jam'iyya su yi fatali da jawabin baya da ya soke ayyukan shugaban riko."
"Idan baku manta ba na miƙa ragamar jagorancin APC a hannun mai girma gwamnan Neja, Abubakar Bello, domin tafiya duba lafiya. Bisa haka, duk matakan da ya zartar a wannan lokacin suna nan."

A wani labarin na daban kuma dan majalisa da Shugabannin APC na tsagin Ministan Buhari sun sauya sheƙa daga jam'iyyar APC

Kara karanta wannan

Da kudin bashi zamu biya kullin tallafin mai: Ministar kudi ta jaddada

Wasu shugabannin APC na tsagin ministan yaɗa labarai, Alhaji Lai Muhammed, sun tabbatar da ficewarsu daga APC.

Sakataren kuɗi na tsagin, Tajuddeen Mohammed, ya ce a halin yanzun ba su yanke jam'iyyar da zasu koma ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel