Da Duminsa: Kwamitin APC Na Riko Da Buni Ke Jagoranci Ta Sallami Sakatarenta, Ta Kada Kuri'ar Rashin Gamsuwa

Da Duminsa: Kwamitin APC Na Riko Da Buni Ke Jagoranci Ta Sallami Sakatarenta, Ta Kada Kuri'ar Rashin Gamsuwa

  • Kwamitin jam'iyyar APC na rikon kwarya da shirya taron kasa, CECPC, ta sanar da kada kuri'ar rashin gamsuwa kan sakatarenta, Sanata Udoedehe
  • Mambobin kwamitin guda 10 cikin 12 ne suka rattaba hannu a kan takardar kuri'ar na rashin gamsuwa da Udoedehe hakan kuma na nufin ya rasa matsayinsa
  • An hasashen cewa wannan korar da aka yi wa Udoedehe ba za ta rasa nasaba da wasikar da Shugaba Buhari ya aike wa CECPC ba inda ya ce akwai bukatar sauya wasu shugabanninta

Kwamitin APC na rikon kwarya da shirya taron jam'iyya, CECPC, a ranar Talata 8 ga watan Maris na 2022, bisa mambobi masu rinjaye ta kada kuri'ar rashin gamsuwa kan sakataren kwamitin, rahoton Vanguard.

Sanarwar ya ce mambobi 10 cikin 12 na kwamitin sun rattaba hannu cikinsu har da Sanata Ken Nnamani, Gwamna Abubakar Sani Bello, Sanata Yusuf Abubakar Yusuf, Prof Tahir Mammah, Sanata Abba Alli, H.E David Lyon, Hon Akinremi Olàide, Mrs Stella Okotete, Barr Ismaeel Ahmad da Dr James Lalu.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Ku bari Buni ya gudanar da taron gangamin jam'iyyar APC, Buhari ya aike da wasika

Da Duminsa: Kwamitin APC Na Riko Da Buni Ke Jagoranci Ta Sallami Sakatarenta, Ta Kada Kuri'ar Rashin Gamsuwa
Kwamitin APC Na Riko Da Buni Ke Jagoranci Ta Sallami Sakatarenta, Ta Kada Kuri'ar Rashin Gamsuwa. Hoto: Vanguard
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kwamitin ta bayyana cewa korar Sanata Udoedehe ya yi dai-dai da sashi na 17, karamin baka na 5 na kudin tsarin mulkin jam'iyyar All Progressives Congress, APC, wadda ya bawa kwamitin wucin gadi kada kuri'ar rashin gamsuwa kan wani mamba da aka samu da laifi.

Idan za a iya tunawa Sanata Udoedehe bai hallarci mafi yawan tarukan da CECPC din na APC ta yi ba a baya-bayan nan kuma hakan ba zai rasa nasaba da wannan sanarwar ta ranar 8 ga watan Maris ba.

Tsige Sanata Udoedehe a matsayin sakataren CECPC ba zai rasa nasaba da wasikar Buhari ba

Akwai alamun wasikar da Shugaba Muhammadu Buhari ya aike wa Shugaban kungiyar gwamnonin APC, Mai Girma Sanata Abubakar Bagudu inda ya ce akwai yiwuwar bukatar sauya wasu shugabannin kwamitin domin cimma burinsa yana da nasaba da wannan.

Kara karanta wannan

Buhari ya amince da sake fasalin hukumar yada labarai ta NBC

Sanarwar na nufin daga yanzu an tsige sakataren kwamitin daga mukaminsa kuma za a nada wani mamba domin maye gurbinsa. Hakan kuma na nufin idan Sanata Udoedehe ya cigaba da gabatar da kansa a matsayin sakataren ba shi da goyon bayan doka.

Saurari karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164