Buhari ya amince da sake fasalin hukumar yada labarai ta NBC

Buhari ya amince da sake fasalin hukumar yada labarai ta NBC

  • Ministan labarai, Lai Mohammed, ya ce Shugaba Buhari ya amince a sake fasalin hukumar yada labarai ta NBC
  • Bashir Bolarinwa ne sabon shugaban kwamitin gudanarwa na hukumar ta NBC
  • An tattaro cewa an zabi mambobin kwamitin ne daidai da tanadin dokar hukumar yada labaran ta kasa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da sake fasalin kwamitin gudanarwa ta hukumar yada labarai ta kasa (NBC).

Hakan ya biyo bayan karewar wa’adin tsohon kwamitin, jaridar The Cable ta rahoto.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, 16 ga watan Maris, ministan labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya ce Bashir Bolarinwa ne sabon shugaban kwamitin.

Buhari ya amince da sake fasalin hukumar yada labarai ta NBC
Buhari ya amince da sake fasalin hukumar yada labarai ta NBC Hoto: Lai Mohammed
Asali: Twitter

Ya ce wani wakilin rundunar tsaro ta farin kaya (DSS), wani wakilin ma’aikatar labarai da al’adu da kuma darakta janar na hukumar suma mambobi ne a kwamitin.

Kara karanta wannan

Kaduna: Baya ga hari a masallaci, 'yan bindiga sun hallaka mutane, sun sace wasu mata

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar ministan, mambobin kwamitin suna wakiltan ra’ayoyi daban-daban kamar yadda dokar NBC ta tanada.

Sauran mambobin sune Wada Ibrahim, Iheanyichukwu Dike, Adesola Ndu, Olaniyan Badmus, Bashir Ibrahim, Obiora Ilo, Ahmad Sajo da Bayo Erikitola.

Lai ya kara da cewar hukumar na da wa’adin shekaru uku, rahoton The Guardian.

A watan Agustan 2020 ne Mohammed ya kaddamar da lambar watsa labarai ta kasa ta shida, duk da adawa daga masu ruwa da tsakin masana'antar.

Daya daga cikin gyare-gyaren da aka yi wa kundin shi ne kari a tarar da ake cin masu kalaman batanci daga N500,000 zuwa naira miliyan 5 da sauransu.

Jerin kudurori 8 da suka tsallaka karatun farko a zauren majalisar wakilai

A wani labari na daban, mun ji cewa wasu kudurori takwas sun tsallaka karatun farko a zauren majalisar wakilai a ranar Laraba, 16 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

2023: Kwankwasiyya da 'Yan kungiyar TMN za su narke a cikin jam'iyyar NNPP

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da majalisar ta fitar a shafinta na Twitter inda ta jero kudirorin da suka tsallake wannan matakin.

Majalisar ta kuma bayyana mambobinta da suka dauki nauyin kudirorina matsayin; Hon. Mohammed Saidu Bargaja, Hon. Musa Agah Avia, Hon. Toluope Akande Sadipe, da kuma Hon. Olusola Steve Fatoba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel