Yadda Mai Mala Buni da shugabannin APC suke fama da shari’a fiye da 200 a gaban kotu

Yadda Mai Mala Buni da shugabannin APC suke fama da shari’a fiye da 200 a gaban kotu

  • Jam’iyyar APC mai mulki ta na da kara sama da 200 da za ta amsa a halin yanzu a gaban Alkali
  • Wasu daga ciki na kalubalantar sahihancin kwamitin CECPC da aka kafa bayan ruguza NWC a 2020
  • Wadannan shari’a za su iya jawo a dakatar da gudanar da zaben shugabannin jam’iyya na kasa

Abuja - Punch ta ce daga cikin karar da aka kai jam’iyyar APC mai mulki a kotu, akwai na yunkurin soke zabukan da aka yi a jihohi da kananan hukumomi.

Masu kalubalantar APC su na ganin tun farko kwamitin CECPC na Mai Mala Buni bai da hurumin shirya zabe a matakin jiha, kananan hukumomi ko ma a mazabu.

Wani hadimin gwamnan jihar Yobe, Yusuf Ali ya shaidawa jaridar Punch wannan a wata hira.

Kara karanta wannan

Kafin a je ko ina, sabon shugaban APC ya zaftare ‘yan kwamitin zabe, daga 1200 zuwa 107

Bayanin hadimin shugaban rikon na jam’iyyar APC wanda yanzu aka ce an dakatar daga matsayinsa ya bayyana wannan ne bayan abin da ya biyo baya.

Shari'a 208 a shekara 1

A shekara guda da ta wuce, an kai jam’iyyar APC kotu sau 208. Akwai Alkalan da ake neman su haramtawa kwamitin na CECPC gudanar da gangami na kasa.

Shari’a tara ake yi da uwar jam’iyyar a kan kafa kwamitin rikon kwarya da aka yi. PM ta ce wadanda suka kai irin wannan kara sun hada da Salisu Umoru.

Mai Mala Buni a Aso Villa
Buhari, Mala Buni, Abubakar Sani Bello, da Kayode Fayemi Hoto: @bunimedia
Asali: Twitter

Kwamitin CECPC ya shiga uku

Umoru ya shigar da karar hukumar INEC, jam’iyyar APC da gwamna Mai Mala Buni a shari’a mai lamba FCT/HC/CV/2958/2021 a kotun tarayya da ke Abuja.

Akwai wani Christian Abeh wanda a shari’arsa mai lamba FHC/ASB/CS/59/2021 yake kalubalantar nada Buni a matsayin shugaban rikon APC na kasa.

Kara karanta wannan

Kwadayin 2023, Jonathan, FFK da abubuwa 5 da suka jawowa Buni matsala a tafiyar APC

Sannan akwai Princess Zahrah Mustapha wanda ta je kotu, ta na cewa a matsayinsa na gwamna mai-ci, Mai Mala Buni ba zai iya jagorantar jam’iyyar APC ba.

A karar da Ushie Eneji da wasu mutane 80 suka kai, sun nemi a ruguza kwamitocin rikon kwarya tun daga matakin mazabu, kananan hukumomi, jihohi zuwa kasa.

Zargin El-Rufai a kan Buni

A wata hira da aka yi da shi, Gwamna Nasir El-Rufai ya ce lauyoyin Mai Mala Buni sun nemi kawo cikas a APC domin su na neman hana APC ta shirya zabe.

Malam El-Rufai ya ce gwamnoni APC sun fahimci lauyoyin Buni da wasu masu goyon bayansu suka shirya wannan zagon-kasan, don haka suka dauki mataki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel