Sauya sheka: APC na neman a hana Saraki, Tambuwal, Ortom da sauransu yin takara na shekaru 30 a sabon kara

Sauya sheka: APC na neman a hana Saraki, Tambuwal, Ortom da sauransu yin takara na shekaru 30 a sabon kara

  • Ana ci gaba da fafutuka tsakanin APC da PDP gabannin babban zaben 2023
  • APC na shirin sanya kafar wando daya da wasu tsoffin mambobinta yayin da jam’iyyar mai mulki ke shirin maka su a gaban kotu
  • APC na so a sanyawa mambobinta da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar adawa bayan sun lashe zabe a karkashinta takunkumi

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na shirin kalubalantar sauya shekar gwamnonin Sokoto, Benue da na Edo zuwa jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP).

Jaridar The Nation ta rahoto cewa wannan yunkurin ya biyo bayan hukuncin da wata babbar kotun tarayya ta yanke na tsige Gwamna Dave Umahi daga kujerarsa saboda ya sauya sheka zuwa APC bayan an zabe shi a karkashin inuwar PDP.

Sauya sheka: APC na neman a hana Saraki, Tambuwal, Ortom da sauransu yin takara na shekaru 30 a sabon kara
Sauya sheka: APC na neman a hana Saraki, Tambuwal, Ortom da sauransu yin takara na shekaru 30 a sabon kara Hoto: Abubakar Bukola Saraki
Asali: Facebook

APC na ganin za ta fi cin riba idan har aka aiwatar da irin haka a kan gwamnonin da wasu shugabannin PDP da aka zaba a karkashin inuwarta.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Makusantan Kwankwaso sun lallaba sun gana da Shekarau, suna kokarin sake jawo shi PDP

Tambuwal, Ortom, Obaseki da Saraki za su fuskanci shari’a

Aminu Tambuwal, Samuel Ortom da Godswin Obaseki duk sun sauya sheka zuwa PDP bayan an zabe su a karon farko karkashin dandamalin jam’iyyar APC.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An kuma tattaro cewa za a jona tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki a cikin karar.

Jam’iyyar na neman a haramtawa Saraki yin takarar kowani matsayi na tsawon shekaru 30 saboda ya sauya sheka bayan lashe zabe a karkashin jam’iyyar APC.

Da take tabbatar da ci gaban, wata majiya a jam’iyyar ta ce an sanar da tawagar lauyoyi amma matakin ya samu tsaiko saboda rikicin shugabanci da ya dabaibaye jam’iyyar mai mulki, rahoton Thisday.

Majiyar ta ce:

“Da gaske ne jam’iyyar na kokarin daukaka kara a kan wasu gwamnoni da suka sauya sheka daga jam’iyyarmu zuwa PDP mai adawa. Da matakin ya dade da farawa idan ba don rikicin shugabanci ba.

Kara karanta wannan

Lawan, Goje, Amaechi Da Sauran Ƴan Siyasa 4 Da Ake Damawa Da Su Tun 1999

“Ina iya fada maku cewa mun kammala tattaunawa da tawagar lauyoyi, da zaran an sulhunta rikicin shugabanci da ke gudana, muna sa ran fara daukar mataki.”

2023: Kungiyar kudu maso gabas ta bayyana abun da zai faru idan dan Igbo bai gaji Buhari ba

A wani labari na daban, wata kungiya mai suna Equity Movement Turn by Turn ta bayyana cewa yankin kudu maso gabas zai balle daga Najeriya idan dan kabilar Igbo bai gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari ba.

Kungiyar ta roki daukacin tsoffin shugabannin kasar da masu ci a yanzu da kada su bari kujerar shugaban kasar Najeriya na gaba ya kubcewa kabilar Igbo, Independent ta rahoto.

A cewar kungiyar, akwai alamu da ke nuna cewa yan Igbo na iya ficewa daga kasar, idan ba a bari sun karbi mulki a 2023 ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel