2023: Shugabannin PDP za su yi taro a kan yadda za a fito da 'Dan takarar shugaban kasa

2023: Shugabannin PDP za su yi taro a kan yadda za a fito da 'Dan takarar shugaban kasa

  • Shugabannin majalisar NEC na jam’iyyar PDP za su yi wani muhimmin taro a farkon makon nan
  • Haka zalika jagororin jam’iyyar adawar za su yi zama duk a kan batun yankin da za a kai takara
  • Ana sa rai a karshen wannan taron, a san daga ina ‘dan takarar PDP a zaben shugaban kasa zai fito

Abuja - ‘Yan siyasar da suke sha’awar neman takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar hamayya ta PDP za su saurari zaman da za ayi a makon nan.

Jaridar This Day ta ce a ranar Talata ne shugabannin jam’iyyar PDP za su yi zama. A nan ne za a fitar da matsaya a kan yankin da za a ba takara a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Sauya sheka: APC na neman a hana Saraki, Tambuwal, Ortom da sauransu yin takara na shekaru 30 a sabon kara

Shugabannin majalisar zartarwa ta PDP za su yi wannan taro ne a ranar Talata. A halin yanzu an fara aika takardar gayyata. The Guardian ta kawo wannan rahoto.

Shugabannin babbar jam’iyyar adawar za su tattauna a kan yiwuwar a warewa wani yanki tutar takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa, ko a bar kofa a bude.

Rahoton Bala Mohammed

Kwamitin da Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ya jagoranta a 2021, ya ba uwar jam’iyya shawarar cewa ta bada dama duk mai sha’awa ya nemi takara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoton kwamitin Bala Mohammed shi ne babban abin da za a tattauna a kai a wajen taron majalisar NEC da kuma taron jagororin PDP na kasa da za ayi.

Shugabannin PDP
Shugabannin PDP a taron NEC Hoto: netxclusive.com
Asali: UGC

Wadannan bangarori biyu na shugabannin majalisar zartarwa da jagorori daga fadin kasar nan za su tafka muhawara a kan shawarar da kwamitin ya gabatar a 2021.

Kara karanta wannan

Kungiyar ASUU ta cigaba da yajin-aiki, za a kara wasu watanni ba a bude jami’o’i ba

Za a zauna da BOT da Gwamnoni

Bayan an yi wadannan taron, shugabannin jam’iyyar za su dauki maganar zuwa gaban majalisar amintattu na BoT domin jin ra’ayinsu kafin a dauki wata matsaya.

Rahoton ya ce bayan haka, za a zauna da gwamnoni da ‘yan PDP a majalisa kafin a yanke hukunci.

Ana rikici a kan kujera a PDP

A daidai wannan lokaci kuma, This Day ta ce an samu sabani tsakanin gwamnonin PDP a kan wanda za a ba kujerar Darektan shirye-shirye na jam’iyya na kasa.

Ofishin wannan darektan ne yake da alhakin zaben ‘yan jam’iyya da za su kada kuri’a wajen fito da ‘dan takarar shugaban kasa, don haka kowa yake hangen kujerar.

Osinbajo ya shigo takara a APC

Mu na jin kishin-kishin cewa Mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya dauki mataki a game da takara a zaben 2023 a karkashin jam'iyyar APC.

Yemi Osinbajo ya sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari shirin takararsa. Hakan yana nufin Osinbajo zai goge raini da tsohon mai gidansa, Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Za a kafa bangarorin siyasa na musamman a duk reshen cocin da Osinbajo yake aikin Fasto

Asali: Legit.ng

Online view pixel