Gwamna Obaseki na nan daram a PDP, mun riga mun yi ram da shi, Ayu

Gwamna Obaseki na nan daram a PDP, mun riga mun yi ram da shi, Ayu

  • Shugaban PDP na ƙasa ya kori duk wani raɗe-raɗin dake yawo cewa gwamnan Edo zai fice daga jam'iyyar ya koma APC
  • Sanata Ayu ya ce ba inda gwamna Obaseki zai je, kuma PDP zata kafa kwamitin da zai magance saɓanin dake cikin PDP a jihar
  • Gwamna Obaseki ya ce PDP ta kammala shirin lashe zaben shugaban kasa, amma irin waɗan nan rikice-rikicen ka iya dakatar da nasarar

Edo - Shugaban babbar jam'iyyar hamayya PDP ta ƙasa, Sanata Iyocha Ayu, ya ce jam'iyyar ta riga ta kama gwamna Obaseki.

Daily Trust ta rahoto cewa gwamnan Edo ya sauya sheƙa daga APC zuwa PDP a lokacin da takaddama ta shiga tsakaninsa da tsohon shugaban APC, Kwamaret Adams Oshiomhole.

Kara karanta wannan

Wajibi APC ta fita tsara a cikin jam'iyyu, Bola Tinubu ya yi magana kan rikicin shugabancin APC

Jam'iyyar PDP ta daga masa kafa ya sake neman tazarce a zaben Edo da ya gabata, kuma ya samu nasara, sai dai a yanzun gwamnan na fama da rashin jituwa da wasu shugabannin PDP a Edo.

Shugaban PDP, Sanata Ayu
Gwamna Obaseki na nan daram a PDP, mun riga mun yi ram da shi, Ayu Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Da yake jawabi a zagayen neman sulhu, Ayu ya ce jam'iyyar PDP ta rasa mulkin Edo tun 2008 saboda rikicin dake tsakanin tsagin marigayi Tony Anenih da na Lucky Igbinedion.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya gargaɗi mabobin jam'iyya a jihar Edo da cewa irin wannan rikicin na cikkn gida ka iya sa PDP ta sake rasa mulkin jihar.

Shugaban ya ce:

"Jam'iyya zata kafa kwamitin da zai sasanta faɗan dake tsakani kuma zamu tabbatar gwamna ya cigaba da kasancewa tare da mu. Obaseki ba zai je ko ina ba, muna riƙe da shi, kuma ta hanyarsa zamu haɗa kan PDP."

Kara karanta wannan

Kwadayin 2023, Jonathan, FFK da abubuwa 5 da suka jawowa Buni matsala a tafiyar APC

"Kada ku bar kowaye ya yaudare ku, Obaseki ba zai bar PDP ba. Yan Najeriya za su ga yadda zamu karbi mutane daga sauran jam'iyyu, a 2023 kuma mu koma kan mulki."
Ya kamata mutanen Edo su yi koyi da jihata Benuwai, idan kuka yi faɗa zaku sha ƙasa a zaɓe, zamu turo tawagar da zata sasanta rikicin Edo. Ina kokari ta bayan fage."

Zamu taimaka PDP ta kwace mulkin Najeriya - Obaseki

A nasa jawabin, Gwamna Obaseki ya ce jihar Edo zata yi duk me yuwuwa har PDP ta lashe kujerar shugaban kasa, domin ita kaɗai ce zata ceci Najeriya.

Gwamnan ya ce:

"Abu ɗaya da zai iya zama mana karfen kafa shi ne rikicin PDP a Edo, matuƙar aka kawo ƙarshen shi da sauran na jihohi, zamu kwace mulki a 2023."

A wani labarin kuma yayin da APC ke fama da rikicin cikin gida, Gwamna Buni, Malami da gwamnan CBN sun dira Landan zasu sa labule da Buhari

Kara karanta wannan

Har yanzun APC ce zabi nagari kuma zata lashe zaben shugaban ƙasa a 2023, Malam El-Rufa'i

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa Mala Buni mai barin gado ya canza tunani, daga Dubai duba lafiya zai wuce Landan ya gana da Buhari.

Rahoto ya nuna cewa Buni zai gana da Buhari ne domin jin abinda ke faruwa daga bakinsa kan zancen tsige shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel