Sauya Sheƙa: Tamkar Ebonyi, PDP a Zamfara Tana Son Kotu Ta Kwace Kujerar Matawalle Ta Bawa Tsohon Mataimakinsa

Sauya Sheƙa: Tamkar Ebonyi, PDP a Zamfara Tana Son Kotu Ta Kwace Kujerar Matawalle Ta Bawa Tsohon Mataimakinsa

  • Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a Jihar Zamfara tana neman kotu ta maye gurbin Matawalle da tsohon mataimakinsa Mahdi Aliyu
  • Jam'iyyar ta PDP ta bakin lauyanta Emmanuel Ukala, SAN, ta ce tunda Gwamna Matawalle ya fice daga PDP ya koma APC, ya rasa kujerarsa
  • Lauyoyi masu kare Gwamna Matawalle da APC karkashin jagorancin Mike Ozekhome (SAN) su kuma sun nemi a basu lokaci domin su yi shiri

Zamfara - Babban kotun tarayya da ke Abuja ta tsayar da ranar 17 ga watan Afrilu don sauraron karar neman tsige Gwamna Bello Matawalle na Jihar Zamfara saboda ficewarsa daga jam'iyyar PDP.

A cikin karar, jam'iyyar PDP ta bukaci kotun ta ayyana tsigaggen mataimakin gwamna Mahdi Aliyu Gusau a matsayin hallastaccen gwamnan Jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Jam'iyyar APC ta kira taron majalisar zartaswa na gaggawa ranar Alhamis

Sauya Sheka: PDP Ta Yunkuro, Za Ta Maye Gurbin Matawalle Da Tsohon Mataimakinsa
Sauya Sheka: PDP Ta Yunkuro, Za Ta Maye Gurbin Matawalle Da Mahdi Gusau. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

PDPn ta kuma bukaci kotun ta kori yan majalisar tarayya da na jiha kimanin 37 da suka koma jam'iyyar APC, rahoton Daily Trust.

Mai shari'a Inyang Ekwo a ranar Alhamis ya tsayar da ranar sauraron shari'ar ne bayan lauyoyin da suka shigar sun bukaci a gwamutsa kararrakin.

Lauyoyin wadanda aka yi kara, karkashin Mike Ozekhome (SAN) su kuma sun nemi a basu lokaci domin su shirya martaninsu kan karar.

Kotu Ta Ƙwace Kujerar Gwamna Da Mataimakinsa Saboda Sauya Sheƙa Daga Jam'iyyar PDP Zuwa APC

Babban kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, a ranar Talata, a kori Gwamna David Umahi na Jihar Ebonyi da Mataimakinsa Dr Eric Kelechi Igwe, bayan sun fice daga jam'iyyar PDP sun koma APC mai mulkin sa, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Jerin Shugabanni jam'iyya 4 da aka fitittika daga ofis karfi da yaji

Kotun, a hukuncin da Mai sharia Inyang Ekwo, ya yi, ta ce kuri'u 393,042 da Gwamna Umahi ya samu a zaben ranar 6 ga watan Maris na gwamnan Jihar Ebonyi, na jam'iyyar PDP ne kuma doka bata amince a mayarwa APC ba.

A cewar kotun, bayan komawa jam'iyyar APC, Umahi da mataimakinsa, ba PDP kadai suka bari ba, sun raba kansu da kuri'un jam'iyyar ta PDP, Daily Trust ta rahoto.

Gwamna Umahi Ya Yi Martani Kan Ƙwace Masa Ƙujera Da Kotu Ta Yi, Ya Bayyana Matakin Da Zai Ɗauka

A martaninsa, Gwamnan Jihar Ebonyi Dave Umahi ya ce zai daukaka kara bisa hukuncin da Babban Kotun Tarayya ta yanke a Abuja na kwace masa kujerarsa saboda komawa jam'iyyar APC, rahoton BBC Pidgin.

A ranar Talata, Babban Kotun na Abuja ta ayyana cewa sauya shekar da Gwamna Umahi da Mataimakinsa Kelechi Igwe suka yi ya saba doka, da kundin tsarin mulki.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya yi babban Kamu, wasu shugabannin PDP sun yi murabus, za su koma NNPP

Mai shari'a Inyang Ekwo ne ya yi wannan hukuncin bisa karar da PDP ta shigar na neman a cire gwamnan da mataimakinsa daga ofishinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel