Komawa APC: Gwamna Umahi Ya Yi Martani Kan Ƙwace Masa Ƙujera Da Kotu Ta Yi, Ya Bayyana Matakin Da Zai Ɗauka

Komawa APC: Gwamna Umahi Ya Yi Martani Kan Ƙwace Masa Ƙujera Da Kotu Ta Yi, Ya Bayyana Matakin Da Zai Ɗauka

  • Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi ya yi martani bayan hukuncin kotun tarayya da ta kwace kujerarsa saboda ficewa daga PDP zuwa APC
  • Umahi, yayin taron manema labarai ya ce kotun ba za ta iya kwace masa kujerarsa ba kuma zai daukaka kara zuwa kotu na gaba don kwato hakkinsa
  • Kotun, yayin hukuncinta a yau Talata ta ce kuri'un da Gwamna Umahi da mataimakinsa suka samu yayin zabe na PDP ne don haka ba su da hurumin cigaba da zama a kujerar bayan komawa APC

Gwamnan Jihar Ebonyi Dave Umahi ya ce zai daukaka kara bisa hukuncin da Babban Kotun Tarayya ta yanke a Abuja na kwace masa kujerarsa saboda komawa jam'iyyar APC, rahooton BBC Pidgin.

Kara karanta wannan

Karin bayani: PDP ta mika sunayen masu maye gurbin gwamnan APC da mataimakinsa da aka tsige ga INEC

A ranar Talata, Babban Kotun na Abuja ta ayyana cewa sauya shekar da Gwamna Umahi da Mataimakinsa Kelechi Igwe suka yi ya saba doka, da kundin tsarin mulki.

Kowawa APC: Gwamna Umahi Ya Yi Martani Kan Ƙwace Masa Ƙujera Da Kotu Ta Yi, Ya Bayyana Matakin Da Zai Ɗauka
Kowawa APC: Gwamnan Ebonyi Ya Yi Martani Kan Ƙwace Masa Ƙujera Da Kotu Ta Yi, Ya Bayyana Matakin Da Zai Ɗauka. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

Mai shari'a Inyang Ekwo ne ya yi wannan hukuncin bisa karar da PDP ta shigar na neman a cire gwamnan da mataimakinsa daga ofishinsu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kotu ba za ta iya kwace min mulki ba, zan daukaka kara, Gwamna Umahi

Amma, yayin jawabin da gwamnan ya yi yayin taron manema labarai, gwamnan ya ce kotu bata da ikon cire shi daga ofishinsa.

Gwamna Dave Umahi da mataimakinsa Kelechi Igwe sun fice daga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ne sun koma APC a shekarar 2020.

Bayan ficewarsu, wasu yan majalisar jihar da mataimakin gwamna suka fice daga PDPn suka bi sahun gwamnan zuwa APC.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta maida zazzafan martani kan tsige gwamnan Ebonyi da ya sauya sheka daga PDP

Kotu Ta Ƙwace Kujerun Ƴan Majalisa 16 Saboda Ficewa Daga PDP

Hakazalika, Babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta kori ‘yan majalisar Jihar Ebonyi guda 17 wadanda suka bar PDP zuwa jam’iyyar APC, daga mukaman su, Vanguard ta ruwaito.

A ranar 17 ga watan Nuwamban shekarar 2020, Gwamna David Umahi da mataimakin sa, Dr Eric Kelechi Igwe suka koma APC.

A hukuncin da kotu ta yanke bisa alkalancin Justice Inyang Ekwo, ta yi nazari akan yadda ‘yan majalisar suka bar jam’iyyar da aka zabe su zuwa wata, hakan yasa kotu ta hana su komawa wata jam’iyyar da kuru’un wata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel