Yanzu-yanzu: Jam'iyyar APC ta kira taron majalisar zartaswa na gaggawa ranar Alhamis

Yanzu-yanzu: Jam'iyyar APC ta kira taron majalisar zartaswa na gaggawa ranar Alhamis

  • Kamar yadda El-Rufa'i ya bayyana ranar Laraba, jam'iyyar APC ta aika sakon gayyatar zaman majalisar zartaswarta
  • Majalisar zartaswar jam'iyya ce ke da hakkin yanke shawari na karshe kan abubuwan da suka shafi shugabancin jam'iyyar
  • Wannan na zuwa ne bayan tunbuke Mai Mala Buni wanda aka yiwa zargin kokarin ha'intar jam'iyyar

Jam'iyyar All Progressives Congress APC ta kira taron majalisar zartaswa na gaggawa ranar Alhamis, 17 ga watan Maris a hedkwatarta dake birnin tarayya Abuja.

Jam'iyyar ta gayyaci dukkan mambobin majalisar zartaswan a wasikar da ta saki da safiyar nan a shafinta na Tuwita.

Mambobin majalisar sun hada da Shugaban kasa, Muhammadu Buhari; mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, dukkan Gwamnonin jam'iyyar APC, Sanatoci da sauran masu ruwa da tsaki.

Jam'iyyar APC
Yanzu-yanzu: Jam'iyyar APC ta kira taron majalisar zartaswa na gaggawa ranar Alhamis Hoto: Presidency
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Borno: Sojoji Sun Gasa Wa Ƴan Ta'adda Aya A Hannu, Sun Kashe 10 Sun Ƙwato Bindigu Masu Harbo Jiragen Sama

Wasikar na dauke da sa hannun Shugaban jam'iyyar APC kuma gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello; Senata Ken Nnamani (wakilin yankin kudu maso gabas), Sanata Yusuf Yusuf (wakilin majalisar dattawa), da Stella Okotete (wakiliyar mata).

Sauran sune Sanata Abba Ali (wakilin Arewa maso yamma), Farfesa Tahir Mamman (wakilin Arewa maso gabas), Barista Isma'il Ahmed (Wakilin matasa).

A cewar wasikar:

"Kwamitin rikon kwaryan jam'iyyar APC a zamanta na ranar 8 ga Maris, 2022 tayi kira ga zaman majalisar zartaswa don tattauna lamarin taron gangami, shugabancin jam'iyya da wasu abubuwa."
"An shirya taron ranar Alhamis, 17 ga Maris, 2022 misalin karfe 11 na safe ta yanar gizo."

Buni ya je ganin likita ne, sai ya ce Bello ya hau kujerarsa kafin ya dawo inji Gwamnan APC

Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi ya ce takwaransa watau Mai Mala Buni shi ne shugaban rikon kwarya na jam’iyya APC mai mulki na kasa.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Wasikar Mai Mala Buni ta karyata kalaman Nasir El-Rufa'i

A ranar Laraba, 9 ga watan Maris 2022, Jaridar Daily Trust ta rahoto David Umahi yana cewa har gobe, jam’iyyar APC ta na hannun su gwamna Mai Mala Buni.

Mai girma gwamnan na Ebonyi ya yi wannan bayani ne yayin da wasu magoya baya suka je yi masa Allah ya kyauta bayan kotu ta tsige shi daga kan mulki.

A nan ne gwamnan ya shaida masu cewa Gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello ya hau kujerar APC ne kurum saboda Mai Mala Buni yana kasar waje a yanzu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel