Kwankwaso ya yi babban Kamu, wasu shugabannin PDP sun yi murabus, za su koma NNPP

Kwankwaso ya yi babban Kamu, wasu shugabannin PDP sun yi murabus, za su koma NNPP

  • Wasu kusoshin jam'iyyar PDP a karamar hukumar Rano ta jihar Kano sun yi murabus daga kan mukamansu da nufin bin Kwankwaso
  • Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, yace zai bar PDP kafin karshen watan Maris, alamu sun nuna zai koma NNPP
  • Tsohon sanatan Kano ta tsakiya ya jagoranci kafa wata ƙungiyar da suka raɗa wa TNM da nufin gyara siyasar Najeriya

Kano - Shugabannin gundumomi da wasu jagororin jam'iyyar APC a ƙaramar hukumar Rano, jihar Kano, sun yi murabus daga kujerunsu.

Jiga-Jigan PDP a yankin sun tabbatar da aje aikin su ne ta wasikun murabus daban-daban da suka aike wa shugaban PDP na ƙaramar hukuma ranar Talata, kamar yadda Premium Times ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Kwankwasiyya da 'Yan kungiyar TMN za su narke a cikin jam'iyyar NNPP

Mutanen da suka ɗauki wannan matakin sun bayyana cewa sun yi haka ne bisa bin sawun tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, na ficewa daga PDP.

Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso
Kwankwaso ya yi babban Kamu, wasu shugabannin PDP sun yi murabus, za su koma NNPPP Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton cewa Kwankwaso zai fice daga jam'yyar PDP a wannan watan na Maris, kuma alamu sun nuna cewa jam'iyyar NNPP Ya dosa.

Yusuf Bala-Usman, shugaban yan tawagar 'Kwankwaso kafarka kafarmu' wanda ya yi magana a madadin tawagarsu, yace sun bar PDP ne saboda rashin adalcin da ake musu a Arewa ta yamma.

Daily Trust ta rahoto Mista Bala Usman, a takardar murabus ɗinsa, ya rubuta:

"Mun aje mukamin mu da mamban PDP saboda rashin demokaraɗiyya tun daga matakin gunduma zuwa matakin ƙasa musamman a shiyyar mu ta arewa maso yamma."

Mutum nawa ne suka fice daga PDP kuma ina suka nufa?

Kara karanta wannan

Ba na shirin sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC, Mataimakin gwamna ya magantu

Bala Usman wanda ya aje mukamin ma'aji a PDP, ya ce zasu bi sawun Kwankwaso zuwa kowace jam'iyya ya koma saboda sun yarda da shi.

Akalla shugabannnin PDP na gundumomi 10 da wasu kusoshin jam'iyya suka yi murabus daga muƙamansu domin bin Kwankwaso.

A wani labarin kuma Jam'iyyar APC ta maida zazzafan martani kan tsige gwamnan Ebonyi da ya sauya sheka daga PDP

Jam'iyyar APC ta bayyana rashin jin daɗinta bisa abinda ta kira cin mutuncin kundin mulki a hukuncin da Kotu ta yanke.

Shugaban APC na Ebonyi, ya ce Kotu ba ta da hurumin tsige gwamna ko mataimakinsa kan sauya sheka zuwa wata jam'iyya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel