2023: Nan da kwanaki 200 za a soma yakin neman takara a Najeriya Inji Hukumar INEC

2023: Nan da kwanaki 200 za a soma yakin neman takara a Najeriya Inji Hukumar INEC

  • Hukumar zabe mai cin gashin kai a Najeriya, INEC ta ce nan da kusan watanni shida za a fara kamfe
  • Daga ranar 28 ga watan Satumba za a bada dama domin a fara yakin neman zaben shugaban kasa
  • Zuwa Watan Maris 2023 za a rufe kofar kamfe, a jira ranar zaben jihohi, majalisa da shugaban kasa

Kaduna - A lokacin da aka fara hango hadarin siyasar 2023, hukumar zabe mai zaman kanta watau INEC ta tsaida lokacin da za a soma kamfe a Najeriya.

Jaridar Daily Trust a wani rahoto da ta fitar a ranar Alhamis, ta ce INEC ta sa lokacin da za a fara yakin neman takarar gwamna, majalisa da na shugaban kasa.

Hukumar zabe ta kasa ta ce daga ranar Laraba, 28 ga watan Satumban 2022 za a soma yakin neman zaben shugaban kasa da na kujerun majalisar tarayya.

Kara karanta wannan

Jerin manyan jihohi 5 a Najeriya da suka fi yawan rumfunan zabe

A wannan lokaci ne masu harin kujerar shugaban kasa da masu neman zama Sanatoci da ‘Yan majalisar wakilan tarayya za su fara kamfe a fadin kasar nan.

INEC ta kuma tsaoda ranar 12 ga watan Oktoban 2022 a matsayin lokacin da za a iya fara yawon yakin neman takarar gwamna da na majalisar dokoki a jihohi.

APC Rivers
APC wajen yakin zaben 2019 Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Babbar kwamishinar zabe ta shiyyar Kaduna, Hajiya Asmau Sani Maikudi ta shaidawa manema labarai wannan a lokacin da ta zanta da su a yammacin Laraba.

Yaushe za a gama kamfe?

Da take jawabi a Kaduna, Asmau Maikudi ta bayyana cewa daga ranar 23 ga watan Fubrairun 2023, an rufe yakin zaben ‘yan majalisa da na shugaban kasa.

Haka zalika bayan 9 ga watan Maris 2023, babu ‘dan takarar gwamna ko ‘dan majalisar dokoki da zai cigaba da kamfe. Za ayi kusan watanni biyar ana yakin zabe.

Kara karanta wannan

Sabon shugaban APC ya dauki matakin farko na dunkule jam’iyya kafin Buni ya dawo

Ana cigaba da shirin 2023

Rahoton ya kuma tabbatar da cewa hukumar INEC ta kara adadin rumfunan zabe a Najeriya. Daga rumfuna 5012 da aka yi amfani da su a 2019, yanzu akwai 8012.

A jawabin na jami’ar hukumar zaben, an kuma fahimci mutane su na cigaba da yin rajistar samun katin zabe na kasa. A yanzu mutane 236,855 sun fara yin rajista.

Zuwa farkon makon nan, mutane 84,335 ne kurum suka kammala rajistar samun katin kada kuri’ar.

Ina takarar Osinbajo?

Kwanan nan za a ji ko Yemi Osinbajo zai yi takarar Shugaban kasa ko ba zai yi ba. Mai magana da yawun bakinsa ne ya bayyana halin da ake ciki a makon nan.

Laolu Akande yace kokarin mai gidansa shi ne sauke nauyin da yake kansa, a matsayin mataimakin shugaban kasa, ya agzawa Muhammadu Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel