Sabon shugaban APC ya dauki matakin farko na dunkule jam’iyya kafin Mala Buni ya dawo

Sabon shugaban APC ya dauki matakin farko na dunkule jam’iyya kafin Mala Buni ya dawo

  • Gwamna Abubakar Sani Bello ya sanar da zaman majalisar NEC bayan zama shugaban riko na APC
  • Gwamnan na jihar Neja ya hadu da ‘yan kwamitin CECPC, zai rage yawan ‘yan kwamitin zabe na kasa
  • Zuwa gobe ne ake sauraron dawowar Mai Mala Buni daga kasar waje yayin da aka yi waje da shi

Abuja - A wani yunkuri na tabbatar da zamansa shugaban jam’iyyar APC na rikon kwarya, Abubakar Sani Bello, ya kira taron majalisar koli na NEC.

Jaridar This Day ta ce sabon shugaban kwamitin na CECPC, Gwamna Abubakar Sani Bello ya yi zama na farko da sauran ‘yan majalisarsa na rikon kwarya.

A wajen wannan zaman a majalisar koli watau NEC za a tabbatar da zaman Abubakar Sani Bello shugaban APC. Wannan rahoto ya zo a gidan talabijin Arise.

Kara karanta wannan

Tuna baya a APC: Abubuwan da suka faru har gwamnan Neja ya maye gurbin Buni

Wata majiya ta ce sanarwar za ta ba jam’iyyar damar yin taron NEC nan da kwanaki bakwai.

Babban makasudin wannan zama shi ne yadda za a bullowa zaben shugabanni na kasa. Babu tabbacin cewa za a bijiro da maganar sauke Buni a wajen taron.

Sabon shugaban APC
Abubakar Sani Bello a sakatariyar APC Hoto: @GovNiger
Asali: Twitter

Zaftare yawan kwamitoci

Baya ga haka, Abubakar Sani Bello zai yi kokarin rage yawan kananan kwamitocin da Mala Buni ya kafa domin shirya zaben shugabannin jam’iyyar APC na kasa.

Rahoton ya ce wannan mataki da gwamnan jihar Neja zai dauka zai bada dama a tafi da sauran manyan jam’iyya, gwamnoni da ‘yan majalisa a aikin kwamitocin.

A karkashin jagorancin Buni, an nada mutane kusan 1700 a cikin kwamitocin da za su shirya zabe na kasa. Gwamna Bello yana ganin mutane 200 sun wadatar.

Kara karanta wannan

Sabon rikicin APC: Buhari ya sanya mun albarka – Gwamnan Neja

Sabon shugaban rikon kwaryan yana da ra’ayin cewa akwai bukatar duka kusoshin jam’iyya su sa baki wajen nada kwamitocin, ba a bar aikin ga mutum daya ba.

Mala Buni zai dawo gobe

A daidai wannan lokaci ne kuma ake samun labari cewa zuwa gobe ne ake sa ran dawowar gwamna Mai Mala Buni wanda aka sauke daga shugabancin CECPC.

Alamu na nuna cewa idan tsohon shugaban rikon kwaryan ya dawo Najeriya daga birnin Dubai, zai yi biyayya ga matakin da shugabannin APC suka dauka a jiya.

Buni ne shugaban APC - Akpanudoedehe

A jiya aka ji cewa jam'iyyar APC ta musanya sauyin shugaba, ta ce har yanzu Mai Mala Buni ne yake rike da CECPC, ta ce mutane su yi watsi da labaran da ke yawo.

Sanarwar ta fito ne daga bakin sakataren rikon kwarya, Sanata John James Akpanudoedehe. Ba a dade ba sai aka ga Abubakar Sani Bello a kan kujerar Mai Mala Buni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel