Osinbajo @65: Fadar Shugaban kasa tayi magana a kan 'takarar' Osinbajo a zaben 2023

Osinbajo @65: Fadar Shugaban kasa tayi magana a kan 'takarar' Osinbajo a zaben 2023

  • Laolu Akande ya ce kwanan nan mataimakin shugaban kasa zai bayyana inda ya sa gaba a 2023
  • Hadimin ya ce yanzu aikin da ke gaban Farfesa Yemi Osinbajo shi ne ya taimakawa mai gidansa
  • Ko a gwamnati, ko a coci, ko a kotu, burin Osinbajo ya bautawa al’ummar kasa inji Laolu Akande

FCT, Abuja - Mai girma mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo zai fito ya yi wa Duniya bayani a game da matsayarsa kan zabe mai zuwa na 2023.

Mai magana da yawun mataimakin shugaban Najeriyar watau Laolu Akande ya bayyana haka. Hukumar dillacin labarai na kasa ta kawo wannan rahoton.

Laolu Akande ya zanta da manema labarai a fadar shugaban kasa a ranar Talata jim kadan bayan Osinbajo ya yi hotunan bikin cika shekaru 65 da haihuwa.

Kara karanta wannan

Duk da yana Landan, Buhari ya tuna da Osinbajo yayin da ya cika shekara 65 da haihuwa

Akande ya fadawa ‘yan jarida cewa a halin yanzu Osinbajo yana kokarin taimakawa Muhammadu Buhari ne domin shawo kan matsalolin kasar.

Abin da Laolu Akande ya fada

“Kamar yadda ya fada har zuwa yanzu, kokarinsa shi ne sauke nauyin da aka zabe shi a matsayin mataimakin shugaban kasa, ya taimakawa shugaban kasa.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Abin da ya maida hankali a kai kenan a yanzu, kuma kamar yadda na fada a Twitter, duk yadda ta kasance, (Osinbajo) zai sanar da mutane a hukumance.”
Buhari da Osinbajo a zaben 2019
Shugaba Buhari da Mataimakinsa a Legas a zaben 2019 Hoto: www.stelladimokokorkus.com
Asali: UGC

Burin Osinbajo har kullum

Premium Times ta rahoto Akande yana cewa abin da ya lura da mataimakin shugaban kasar shi ne yana kokarin ganin gwamnati tana da tausayi da adalci.

“Yana yawan fada a wajen taron da muke yi cewa 'mu na wannan wurin ne saboda mutane sun zabe mu.'”

Kara karanta wannan

Sai irin su Buhari: Osinbajo ya bayyana wanda iya zai magance matsalar tsaro a Najeriya

“'Mun zo ne domin kare hakkin mutane', saboda haka shi mutum ne da ya damu da yi wa jama’a hidima”
“Ko yana gwamnati, ko yana Fasto ko a matsayinsa na lauya. Ya fahimci yi wa mutane hidima a rayuwa”
“Kamar yadda ku ke gani, ‘yan Najeriya da-dama su na so a ce irin wannan mutum ke jagorantarsu.”

- Laolu Akande

Buhari ya taya Osinbajo murna

A jiya mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo yake bikin murnar kara shekara. Shugaba Muhammadu Buhari ya aikowa mataimakinsa sakon farin ciki.

Kamar yadda ku ka ji shugaban Najeriyar ya yaba da irin gudumuwar da Yemi Osinbajo yake badawa. Buhari ya bayyana wannan ne ta bakin Femi Adesina.

Asali: Legit.ng

Online view pixel