Buni ya je ganin likita ne, sai ya ce Bello ya hau kujerarsa kafin ya dawo inji Gwamnan APC

Buni ya je ganin likita ne, sai ya ce Bello ya hau kujerarsa kafin ya dawo inji Gwamnan APC

  • David Umahi ya kawo wani sabon kauli a kan rikicin cikin gidan da jam’iyyyar APC ta ke fama da shi
  • Gwamnan jihar Ebonyi ya bayyana cewa har gobe Mai Mala Buni ne shugaban APC na rikon kwarya
  • A cewar David Umahi, Abubakar Sani Bello ya na riko ne kafin Gwamnan Yobe ya dawo daga ketare

Ebonyi - Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi ya ce takwaransa watau Mai Mala Buni shi ne shugaban rikon kwarya na jam’iyya APC mai mulki na kasa.

A ranar Laraba, 9 ga watan Maris 2022, Jaridar Daily Trust ta rahoto David Umahi yana cewa har gobe, jam’iyyar APC ta na hannun su gwamna Mai Mala Buni.

Mai girma gwamnan na Ebonyi ya yi wannan bayani ne yayin da wasu magoya baya suka je yi masa Allah ya kyauta bayan kotu ta tsige shi daga kan mulki.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa a APC, an samu Sanatoci sun ce ba a tunbuke Mala Buni daga matsayinsa ba

A nan ne gwamnan ya shaida masu cewa Gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello ya hau kujerar APC ne kurum saboda Mai Mala Buni yana kasar waje a yanzu.

Rahoton ya ce David Umahi ya yi jawabi ne a garin Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi a jiya. Umahi ya ce a gabansu Buni ya ce Bello ya zama shugaban riko.

Gwamnan Ebonyi
Gwamnan Ebonyi, Dave Umahi Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Jawabin Dave Umahi

“’Ya ‘yan APC, ina so in gode maku, kuma barin in fada maku, babu wani rabuwar kai a jam’iyyar APC.”
“Shugaban APC na rikon kwarya ya tafi hutun ganin likita ne, mu na nan ya ce gwamnan Neja ya rike masa”
“Idan har za a samu wani sauyi, za a sanar da ku, amma zuwa yanzu babu wani canji, babu baraka a APC.” - David Umahi

Kara karanta wannan

Tsige gwamnan Ebonyi: Shehu Sani ya bayyana abun da zai faru da sauran gwamnonin da suka sauya sheka

Martanin El-Rufai

Jim kadan bayan an yi wannan sai aka ji Nasir El-Rufai yana cewa Muhammadu Buhari ya bada umarni ayi waje da Mai Mala Buni, a daura Abubakar Sani Bello.

Nasir El-Rufai ya bayyana cewa gwamnoni 19 ne suka goyi bayan sauke Mala Buni da aka yi, ya ce amma akwai wasu ‘yan tsirarru da ba su goyon bayan hakan.

Da yake magana, Gwamnan na Kaduna ya ce wadannan tsirarru ne suke yada karya a jam’iyyar APC, yana mai tabbatar da cewa Mala Buni ya rasa kujerarsa kenan.

Ra’ayin gwamna Umahi wanda bai dade da shigowa jam’iyyar APC ba ya zo daya da na shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa watau Sanata Yahaya Abdullahi.

Buni ya yi waje

A makon nan ku ka ji abokan aikin Gwamna Mai Mala Buni su ka shirya masa tuggun da aka yi waje da shi. Har gwamnonin da ke tare da shi, sun juya masa baya

Kara karanta wannan

Allah ya ji kanki: Dino Melaye ya yiwa APC ba'a bayan barkewar rikicin shugabanci a jam’iyyar

Shugaban gwamnoni na kasa da shugaban gwamnonin APC su na cikin wadanda suka sa shugaba Muhammadu Buhari ya bada umarni a kori Buni daga CECPC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel