Rikicin gida: Gwamnoni 6 da suka shiga suka fita, har suka ga bayan Mai Mala Buni a APC

Rikicin gida: Gwamnoni 6 da suka shiga suka fita, har suka ga bayan Mai Mala Buni a APC

  • Gwamnonin jihohin APC ne suka yi sanadiyyar da Mai Mala Buni ya rasa kujerar shugaban jam’iyya
  • Wadannan gwamnoni sun yi nasarar gamsar da Shugaban kasa cewa ba a shirin yin zaben shugabanni
  • Sauran gwamnonin da ake ganin su na goyon bayan abokin aikinsu, Mala Buni sun dawo daga rakiyarsa

Abuja - Tunbuke gwamnan jihar Yobe daga kujerar shugaban rikon kwarya na jam’iyyar APC na kasa ya yiwu ne saboda sa hannun gwamnonin jihohi.

Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Talata, 8 ga watan Maris 2022, ta ce abokan aikin Gwamna Mai Mala Buni ne suka sauke shi daga kujerar da yake kai.

Bayan sun yanke shawara tsakaninsu, sai wadannan gwamnoni suka samu ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari, suka kai masa wannan magana.

Majiyar ta bayyana cewa a karshe Mai girma shugaban kasa ya amince da maganar gwamnonin jihohin, sai ya bada umarnin a tunbuke Mai Mala Buni.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa a APC, an samu Sanatoci sun ce ba a tunbuke Mala Buni daga matsayinsa ba

Tun da Shugaba Muhammadu Buhari ya tsoma baki, kwanakin Mala Buni a CECPC suka zo karshe. Buhari ya gamsu da irin hujjojin da aka kawo masa.

Gwamnonin APC
Muhammadu Buhari da Gwamnonin APC Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Su wane gwamnoni ne?

Jaridar ta ce gwamnonin da suka yi wannan aiki za su kai shida, dukkaninsu su na kan wa’adin karshe ne a kan mulki, su na gaba da Mala Buni a matsayi.

Daga cikinsu akwai shugaban kungiyar gwamnoni na kasa da kuma shugaban gwamnonin APC. Mafi yawansu sun fito ne daga Arewa, daya ne daga Kudu.

Gwamnonin su ne na jihohin Ekiti, Jigawa, Filato, Kebbi, Neja da kuma na jihar Kaduna. Daga cikinsu ne aka zabi wanda ya zama shugaban rikon kwarya.

  1. Dr. Kayode Fayemi
  2. Malam Nasir El-Rufai;
  3. Sanata Atiku Abubakar Bagudu
  4. Mohammed Badaru Abubakar
  5. Simon Lalong
  6. Abubakar Sani Bello

Kara karanta wannan

Tuna baya a APC: Abubuwan da suka faru har gwamnan Neja ya maye gurbin Buni

Ragowa sun juya-baya

Wani rahoto da This Day ta fitar ya nuna cewa har gwamnonin da a baya ake tunanin su na tare da Mala Buni, sun yi watsi da shi da tafiya tayi tafiya a APC.

Daga cikinsu akwai; Farfesa Babagana Zulum, Babjide Sanwo-Olu, Yahaya Bello, Sanata Hope Uzondinma, Dapo, Inuwa Yahaya da AbdulRahman Abdulrazaq.

Buni ne yake rike da CECPC har gobe

Sanatocin jam’iyyar APC sun yi zama na musamman a game da rikicin cikin gidan da ya kunno kai, sun ce babu gaskiya a zancen cewa an tsige Mai Mala Buni.

An ji cewa shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Sanata Yahaya Abdullahi ya ce gwamnan Neja ya dare kujera ne kurum saboda shugaban APC ya na jinya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel