Wata sabuwa a APC, an samu Sanatoci sun ce ba a tunbuke Mala Buni daga matsayinsa ba

Wata sabuwa a APC, an samu Sanatoci sun ce ba a tunbuke Mala Buni daga matsayinsa ba

  • Sanatocin jam’iyyar APC sun yi zama na musamman a game da rikicin cikin gidan da ya kunno kai
  • ‘Yan majalisar dattawan sun bayyana cewa babu gaskiya a zancen cewa an tsige Mai Mala Buni
  • Sanata Yahaya Abdullahi ya bayyana wannan, ya ce Abubakar Sani Bello shugaban riko kwarya ne

Abuja - Wasu Sanatocin jam’iyyar APC a majalisar dattawan Najeriya sun yi watsi da rahoton da ke yawo na cewa an sauke Mai Mala Buni daga kujerarsa.

Jaridar Daily Trust a wani rahoto da ta fitar a ranar Talata, ta bayyana cewa Sanatocin su na ganin ba a tsige Mala Buni daga shugaban rikon kwarya ba.

Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Sanata Yahaya Abdullahi ya ce gwamnan jihar Neja ya dare kujera ne kurum saboda shugaban APC ba ya nan.

Kara karanta wannan

Rikicin gida: Gwamnoni 6 da suka shiga suka fita, har suka ga bayan Mai Mala Buni a APC

A cewar Sanatan na Kebbi, Abubakar Sani Bello ya karbi ragamar jam’iyyar APC ne domin ganin gwamna Buni bai da lafiya, kuma har ta kai ya je kasar waje.

Da yake zantawa da manema labarai bayan ya hadu da Sanatocin APC, an rahoto Abdullahi yana cewa rade-radin da suke yawo a Najeriya ba gaskiya ba ne.

Yahaya Abdullahi ya bayyana cewa sun zauna ne saboda halin rikicin da jam’iyyar APC ta shiga.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban APC
Sabon shugaban APC, Abubakar Sani Bello Hoto: GovNiger
Asali: Twitter

Za a rufawa Buni asiri

A daidai wannan lokaci ne mu ke samun rahoto daga This Day cewa ana kokarin neman yadda za ayi waje da Mai Mala Buni daga kan mukaminsa cikin sauki.

Jagororin jam’iyyar APC su na neman hanyar sauke Gwamnan na jihar Yobe daga kujerar shugaban rikon kwarya na kasa ba tare da ci masa mutunci ba.

Kara karanta wannan

Sabon shugaban APC ya dauki matakin farko na dunkule jam’iyya kafin Buni ya dawo

Majiyar ta ce daga cikin hanyoyin da ake tunani za a bi shi ne, a fadawa Buni ya yi murabus daga shugaban kwamitin riko da shirya zabe na kasa watau CECPC.

Za a ba gwamnan shawara ya ajiye aikin da hannunsa da sunan bai da cikakken lafiya. Wata shawara ita ce ya sauka daga mukamin saboda ya nemi tazarce.

Ko da John James Akpanudoedehe ya musanya rahotannin murabus, da wahala su cigaba da rike mukamansu. Buni zai koma jihar Yobe domin ya yi takara a 2023.

Bello ya gyara zama

A makon nan aka ji cewa Gwamna Abubakar Sani Bello ya sanar da zaman majalisar NEC bayan zama shugaban riko na APC, hakan zai ba shi dama ya mike kafafu.

A lokacin da ake san ran dawowar Mai Mala Buni, sai aka ji Gwamnan na jihar Neja ya hadu da ‘yan kwamitin CECPC, zai rage yawan ‘yan kwamitin zabe na kasa.

Kara karanta wannan

Tuna baya a APC: Abubuwan da suka faru har gwamnan Neja ya maye gurbin Buni

Asali: Legit.ng

Online view pixel