Kayar Kifi tayi ajalin DIG Egbunike, babban dan sandan dake binciken Abba Kyari

Kayar Kifi tayi ajalin DIG Egbunike, babban dan sandan dake binciken Abba Kyari

  • Najeriya ta yi rashin daya daga cikin manyan jami'an yan sanda a Najeriya, DIG Joseph Egbunike
  • Joseph Egbunike ya mutu ne bayan garzayawa da shi asibiti cikin gaggawa yayinda yake cin abinci
  • Ana zargin Likitoci sun yi kuskuren yi mata aikin tiyata saboda yana da hawan jini amma suka farkeshi

Abincin karshe da mataimakin Sifeto Janar na yan sanda, Joseph Egbunike, yaci a ofishinsa na FCID ya zama ajalinsa, FIJ ta ruwaito.

Majiyoyi daga cikin hedkwatan yan sanda dake Abuja sun nuna cewa DIG Egbunike na cin abinci a ofishinsa ne ranar Talata sai kayar kifi ta makale masa.

Majiyar tace:

"Yana cin abinci a ofishinsa kayar kifi ta makale masa a makogoro, an yi yunkurin duniya don cire kayar amma abu ya gagara."
"Kawai sai aka garzaya da shi asibiti inda likitoci suka samu nasarar cire kayar bayan aikin tiyata."

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Ba rikicin APC ya damu talaka ba, yan jarida na batawa kansu lokaci kan rikicin APC, Buhari

Majiyar tace bayan cire kayar ya samu sauki kuma ya koma gida. Amma daga baya ya sake komawa asibiti saboda bai jin dadi kuma daga nan ya kwanta dama.

DIG Egbunike
Kayar Kifi tayi ajalin DIG Egbunike, babban dan sandan dake binciken Abba Kyari
Asali: UGC

Wata majiyar ta FIJ wacce ta tabbatar da kai Egbunike asibiti tace:

"Lafiyar jikinsa dama babu karfi saboda kibarsa."

Mutuwar Egunike

Mun kawo muku cewa Jami’in ‘Dan Sandan da ya yi bincike kan Abba Kyari ya mutu kwatsam a ofis

Joseph Egbunike, wanda shi ne Mataimakin Sufeta-Janar mai kula da sashen FCID na rundunar ‘yan sandan Najeriya ya kwanta dama.

Rahoton da ya fito daga Punch a ranar Laraba, 9 ga watan Maris 2022 ya tabbatar da wannan labari.

Kamar yadda mu ka ji, DIG Joseph Egbunike ya fadi ne cikin ofishinsa a yammacin ranar Talata. Tun daga nan bai farfado ba, sai dai aka dauki gawarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel