Bakin alkalami ya bushe: An hana Buhari da Majalisa taba dokar da aka sa wa hannu

Bakin alkalami ya bushe: An hana Buhari da Majalisa taba dokar da aka sa wa hannu

  • Kotun tarayya na Abuja ba ta amince a goge wani sashe a cikin dokar zabe na shekarar 2022 ba
  • Alkalin da ya saurari karar da PDP ta shigar, ya ce ba za a iya taba dokar da aka sa wa hannu ba
  • Mai shari’a Inyang Ekwo ya zartar da wannan hukuncin, za a cigaba da zaman shari’ar a Abuja

Abuja - Babban kotun tarayya mai zama a garin Abuja ta hana shugaba Muhammadu Buhari da wasunsa wasa da sabon dokar zabe da aka shigo da shi.

A ranar Litinin, 7 ga watan Maris 2022, Mai shari’a Inyang Ekwo ya amince da karar da jam’iyyar PDP ta shigar, ya ce ba za a iya wasa da wannan doka ba.

Kara karanta wannan

Babu maganar janye yajin-aiki, kungiyar ASUU ta gindayawa Gwamnatin Najeriya sharadi

Alkalin ya gamsu cewa tun da har kudirin gyaran zaben ya zama doka, ba za a iya kewaya shi ba. Wannan labari ya zo ne a jaridar Daily Trust dazu da safe.

A shari’ar mai lamba ta FHC/ABJ/CS/247/2022, lauyan PDP ya fadawa kotu shugaban kasa bai da hurumin da zai ce sashe na dokar ya sabawa tsarin mulki.

James Onoja SAN ya shigar da kara

Bayan sauraron lauyan da ya tsayawa jam’iyyar PDP a shari’ar watau James Onoja SAN, Alkali ya hana yi wa sashe na 84 na dokar zaben wata kwaskwarima.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Onoja SAN ya kafa hujja da sashe na 228 na kundin tsarin mulki da ya yi bayanin karfin jam’iyyu.

Lauyan ya ce tun da Buhari ya sa hannu a kudirin da aka gabatar masa a ranar 25 ga watan Fubrairu, ba zai iya ba majalisa umarnin cire wani sashe a dokar ba.

Kara karanta wannan

Nadin mukamai ya jawo Lauya ya yi karfin-hali, ya maka Shugaban kasa a gaban Alkali

An takawa Buhari da Majalisa burki

Mai shari’a Inyang Ekwo ya hana shugaban kasa Muhammadu Buhari, Ministan shari’a, shugaban majalisar dattawa da na wakilai da INEC taba wannan dokar.

Rahoton ya ce sauran wadanda wannan hukunci zai shafa sun hada da kakakin majalisar tarayya da mataimakan shugabannin majalisar dattawa da kuma na wakilai.

Wannan hukunci da Alkalin babban kotun tarayyar ya zartar, zai yi aiki ne na wani gajeren lokaci. Za a cigaba da sauraron wannan shari’ar ne a ranar 21 ga wata.

Masu mukamai za su yi murabus?

Ku na da labari cewa dokar zabe za ta taba FEC domin za ta wajabtawa Ministocin shugaba Muhammadu Buhari da suke da burin takara a 2023 su rasa mukamai

Tun tuni dama akwai Ministocin gwamnatin tarayya da masu fashin-baki da nazarin siyasar gida su ke ganin cewa su na harin takarar gwamna ko shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel