Babu maganar janye yajin-aiki, kungiyar ASUU ta gindayawa Gwamnatin Najeriya sharadi

Babu maganar janye yajin-aiki, kungiyar ASUU ta gindayawa Gwamnatin Najeriya sharadi

  • Malaman jami’a sun yi martani a game da matakin da babban Ministan ilmi na tarayya ya dauka
  • Adamu Adamu ya kafa sabon kwamiti da zai duba yiwuwar dabbaka yarjejeniyar da aka yi a 2009
  • Kungiyar ASUU ta hau kujerar na-ki, ta ce dole ne a cika alkawuran da aka riga aka yi mata a baya

Abuja - A ranar Litinin, 7 ga watan Maris 2022, Ministan ilmin Najeriya, Adamu Adamu ya ba kwamitin da ya kafa wa’adin watanni uku ya gama aikinsa.

Nauyin da ke kan wannan kwamiti shi ne duba yarjejeniyar da gwamnatin kasar ta shiga da kungiyoyin ASUU, SSANU, NASU da NAAT a shekarar 2009.

Jaridar Premium Times ta kawo rahoto cewa shugabannin kungiyar malaman jami’a watau ASUU sun nuna ba za su dawo aiki ba sai an cika alkawuran nan.

Kara karanta wannan

Minista ya yi wa daliban jami’a albishir, ASUU ta kusa janye yajin-aikin da ta shiga

Wannan kwamiti mai mutane bakwai zai yi aiki ne a karkashin Nimi Briggs. Wannan labari bai yi wa ASUU dadi ba, ta ce ba za ta yarda da wannan shirin ba.

Ba za ta sabu ba inji Adelaja Odukoya

Shugaban ASUU na reshen Legas, Adelaja Odukoya ya ce matsayar majalisar kolinsu ta NEC ita ce ba za a koma aiki ba har sai an biya masu dukkanin bukatunsu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Adelaja Odukoya ya ce su na nan a kan bakarsu na cewa dole ayi watsi da manhajar IPPIS, a rungumi UTAS. Sannan kuma su na so a gyara albashin malamai.

Babu maganar janye yajin-aiki, kungiyar ASUU ta gindayawa Gwamnatin Najeriya sharadi
Ministan ilmi, Adamu Adamu Hoto: www.thisdaylive.com
Asali: UGC

Odukoya ya ce idan aka cigaba da tafiya a haka, ana nada kwamitin da zai duba yarjejeniyar da aka yi a baya, yajin-aikin da ASUU take yi ba zai taba zuwa karshe ba.

Nawa ne albashin Farfesa?

Kara karanta wannan

Yajin aiki a Jami'o'i: Abubuwan da aka tattauna tsakanin ASUU da FG a taron yau Talata

Jami’in na ASUU ya koka da cewa albashin Farfesa wanda ya kure matakin boko bai wuce N416, 000 ba, ya ce tun 2009 ba a karawa malaman jami’a albashinsu ba.

“Nawa ne buhun shinkafa a 2009, nawa ta ke yanzu? Nawa ne farashin kudin kasar waje a lokacin da yanzu? Albashin ‘yan siyasa bai canza ba tun 2009? – Odukoya.

Ra’ayin Farfesa Abdulgaffar Amoka

Abdulgaffar Amoka wani Farfesa a jami’ar ABU Zaria ya ce tun Disamban 2020 kwamiti ya kammala aiki a game da batun yarjejeniyar da aka sa wa hannu a 2009.

Da yake magana a shafinsa na Facebook, Farfesa Abdulgaffar Amoka ya ce abin da ya ragewa gwamnati shi ne ta dabbaka MoA da aka bata tun a watan Mayun 2021.

Malamin ya nuna idan aka tafi a haka, za a kara shafe wasu watanni uku ana yajin-aiki a jami’o’i.

Babu kudi a kasa - Minista

Ku na sane da cewa Ministan kwadago da ayyuka na tarayya, Sanata Chris Ngige ya bayyana cewa ba su da kudin da ASUU ta ke nema, sai idai idan karya za ayi masu.

Kara karanta wannan

Babu dadi: IGP ya koka kan yadda 'yan sanda ke amfani da makamai ta wasu hanyoyi

Chris Ngige ya fadawa manema labarai cewa a halin yanzu ba su da wadannan biliyoyin. Ngige ya ce inda babbar matsalar ta ke shi ne a game da kudin farfado da jami’o’i.

Asali: Legit.ng

Online view pixel