Nadin mukamai ya jawo Lauya ya yi karfin-hali, ya maka Shugaban kasa a gaban Alkali

Nadin mukamai ya jawo Lauya ya yi karfin-hali, ya maka Shugaban kasa a gaban Alkali

  • Wani Lauya, Francis Mgbo yana kalubalantar shugabannin da aka nada a NMDPRA da kuma NUPRC
  • A ra’ayin lauyan da ya shigar da kara, ba a bi dokar kasa wajen nadin darektoci da shugabannin ba
  • Wannan ta sa Francis Mgbo ya kai karar Ministan shari’a da Ministan man fetur gaban kotu a Abuja

FCT – Abuja, Wata babban kotun tarayya da ke zama a garin Abuja ta ba wani Lauya damar yin shari’a da Mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A wani rahoton da ya fito daga Vanguard a ranar Litinin, an ji Francis Mgbo yana neman kotu ta dakatar da shugaban kasa daga yin wasu nadin mukamai.

Francis Mgbo yana da ta-cewa ne a game da nadin sababbin shugabanni da aka yi a hukumomin NUPRC da NMDPRA masu kula da harkar man fetur a kasa.

Kara karanta wannan

Badakalar kwayoyi: Bayan kwanaki 20 a tsare, za a shiga kotu da Abba Kyari da mutum 6

Mgbo ya roki kotu ta hana a nada shugabanni da darektoci a wadannan hukumomi na tarayya.

Wadanda Francis Mgbo ya hada a karar da ya shigar a Abuja sun hada da Ministan shari’a watau AGF, Ministan harkokin man fetur sai NUPRC da NMDPRA.

Kotu ta karbi rokon Mgbo

The Sun ta ce Alkali mai shari’a Emeka Nwite ya ba wannan lauya damar kalubalantar nadin shugabanni da manyan darektoci da aka yi a hukumomin.

Shugaban kasa
Muhammadu Buhari ne Ministan man fetur Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Emeka Nwite ya tsaida ranar 31 ga watan Maris 2022 a matsayin lokacin da za a saurari shari’ar.

A karar da wannan mutum ya shigar, ya nemi kotu ta tursasawa Ministan fetur, NUPRC da NMDPRA su gabatar da duk bayanan da aka nema a hannunsu.

Lauya ya na neman N10m

Kara karanta wannan

Karin bayani: Kotu ta yi watsi da bukatar Abba Kyari, ta ce ba za a bada belinsa ba

Wannan lauyan ya kafa hujja ne da dokar FOI da sashe na 39 na kundin tsarin mulkin Najeriya.

Mgbo ya nemi Kotu ta sa Ministan man fetur da hukumomin tarayyar biyu su biya shi N10m. Alkali Nwite zai zauna duk a kan wannan idan an soma shari'a.

Mgbo ya ce wadanda aka ba kujerun ba su cancanta ba saboda wasu dalilai, daga ciki akwai zargin zarce shekaru 60 ko kuma ba su da cikakken kwarewar aiki.

Buhari ya wuce Landan

A jiya ne aka ji cewa kafin ya bar Najeriya zuwa Landan, Muhammadu Buhari ya yi magana a game da wanda zai rike kasa da zaben shugabannin da APC za ta yi.

Baya ga Farfea Yemi Osinbajo, Buhari ya ce akwai sakataren gwamnatin tarayya da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa da za su cigaba da aiki ko ba ya nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel