Takara a 2023: Ina neman zaman shugaban ƙasa ne saboda gyara goben 'ya'yan mu, Tinubu

Takara a 2023: Ina neman zaman shugaban ƙasa ne saboda gyara goben 'ya'yan mu, Tinubu

  • Jagoran APC na ƙasa, Asiwaju Bola Tinubu, ya ce yana neman zama shugaban ƙasa ne saboda goben yaran Najeriya dake tasowa
  • Tinubu wanda ya ziyarci jihar Ekiti domin neman goyon baya, ya ce Najeriya na bukatar jagora nagari, da zai haɗa kan ƙasa
  • Matasa sun fito kwansu da kwarkwata suna rera waka da kidan yabo ga jagoran APC na ƙasa tun kafin ya isa

Ekiti - Tsohon gwamnan jihar Legas kuma ɗan takarar shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ranar Alhamis, ya ce Najeriya tana bukatar jagora nagari da zai haɗa kan yan ƙasa.

Punch ta rahoto yana cewa kasar na bukatar wanda zai magance matsalar tsaro. da haɓaka tattalin arziki ta yadda zai amfanar da miliyoyin mutane.

Jagoran jam'iyyar APC na ƙasa ya yi wannan furucin ne a jihar Ekiti, a wani bangare na cigaba da ziyarar neman goyon bayan takararsa a 2023.

Kara karanta wannan

Muna Da Huja Da Ke Nuna PDP Ce Ta Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa a 2019, in Ji Ayu

Bola Tinubu
Takara a 2023: Ina neman zaman shugaban ƙasa ne saboda gyara goben 'ya'yan mu, Tinubu Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Ya ce ya zaɓi fara neman shawarin Sarakunan gargajiya ne kafin ya bayyana kudirinsa sabida girman da yake bai wa al'ada da gargajiya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daily Trust ta rahoto Tinubu ya ce:

"Ina neman takara ne saboda sabun ta kyakkyawan fata da kuma gyara goben yaran mu. Idan muna son Najeriya ta zama tsintsiya kuma ta samu cigaba, wajibi mu yi hakuri da sanin ya kamata."
"Muna bukatar cigaba da haɗa kan mu, domin haka ne hanya ɗaya tilo da ƙasar mu zata samu ɗaukaka."

Yadda mutane suka tarbi Tinubu a Ekiti

Yadda kasan wata ranar bikin al'ada mai matukar muhimmanci a fadar Sarkin Ado Ekiti, Oba Adeyemo Adejugbe. Mutane sun taru suna rera waka suna rawa, suna yabon Bola Tinubu.

Dandazon mutanen iya ganin ido, sun cigaba da rera wakokin yabo ga jagoran APC na ƙasa yayin da suke jiran isowarsa.

Kara karanta wannan

Hadimin Buhari: Zaben 2023 zai fi kowane zabe zama sahihi saboda kokarin Buhari

Tinubu ya isa fadar tare da rakiyar mataimakin gwamnan jihar Ekiti, Bisi Egbeyemi, wanda ya wakilci gwamna Kayode Fayemi.

Kazalika Jagaba ya samu rakiyar kungiyar magoya bayan Tinubu a yankin kudu ta yamma bisa jagorancin Sanata Senator Dayo Adeyeye.

Ɗan takarar shugaban ƙasan ya fara ganawa da majalisar sarakunan gargajiya na jihar Ekiti a babban birnin jihar Ado-Ekiti.

A wani labarin kuma Matar Abdulmalik Tanko ta ba da shaida a Kotu kan kisan Hanifa Abubakar

Matar wanda ake zargi da kashe Hanifa Abubakar, Jamila Muhammad, ta ba da shaida a Kotu bayan ya ce ba shi ya kashe ta ba.

Jamila ta faɗi yadda ya kawo mata yarinyar da kuma karyar da ya mata game da ita, har zuwa ranar da ya ɗauke ta da daddare bayan kwana 5..

Asali: Legit.ng

Online view pixel