Jigon PDP ga Matawalle: Ka daina tursasa mutane don kawai su shiga APC

Jigon PDP ga Matawalle: Ka daina tursasa mutane don kawai su shiga APC

  • Wani jigon PDP, Iyorwuese Hagher, ya bukaci gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle da ya daina razana 'ya'yan jam'iyyar don sun ki komawa APC
  • Iyorwuese ya ce ba a yiwa mutane dole a mulkin damokradiyya
  • Hakan martani ne ga tsige mataimakin gwamnan jihar, Mahdi Gusau da gwamnatin jihar ta yi

Zamfara - Wani jigon jam’iyyar PDP kuma shugaban kwamitin yakin neman zaben shugabancin Bukola Saraki, Iyorwuese Hagher, ya yi kira ga Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara da ya daina razana yan jam'iyyar a jihar don sun ki komawa APC

Iyorwuese wanda ya kasance a garin Gusau, babbar birnin jihar a ranar Talata, don tattaunawa kan takarar shugabancin Saraki ya ce ba za a iya yiwa mutane dole ba a shugabanci, Punch ta rahoto.

Jigon PDP ga Matawalle: Ka daina tursasa mutane don kawai su shiga APC
Jigon PDP ga Matawalle: Ka daina tursasa mutane don kawai su shiga APC Hoto: sunnewsonline.com
Asali: Twitter

Ya ce:

Kara karanta wannan

Daruruwan mambobi a mahaifar dan takarar gwamna na PDP sun sauya sheka zuwa APC

“Zancen gaskiya shine cewa ba za ka iya mulkar mutane ta hanyar tursasawa ba, ba za ka iya shugabantar mutane ta hanyar barazana ko bita da kulli ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ba za ka iya amfani da tsoratarwa a damokradiyya don tursasa mutane zama ‘ya’yan jam’iyyarka ba. Wannan shine abun da gwamnatin APC ke yi a wannan jaha ta Zamfara.
“Muna sane da cewar sau uku gwamnatin APC na son ruguza hedkwatar PDP a Zamfara saboda mataimakin gwamnan bai koma APC tare da gwamnan ba."

Ya nuna rashin jin dadi kan tsige mataimakin gwamna, Mahdi Gusau, daga kujerarsa, inda ya bayyana hakan a matsayin cin mutuncin tsarin shari’a.

A cewarsa, kasar bata ji dadin tsige mataimakin gwamnan da aka yi ba, inda ya kara da cewar yan Najeriya na bayan mutanen Zamfara.

Ya shawarci mutanen jihar da su tabbatar da ganin cewa an zabi masu mutunci a babban zaben 2023.

Kara karanta wannan

Zamfara: Bayan tsige mataimakin gwamna, majalisa ta maye gurbinsa da sanata

Tsohon shugaban majalisa ya takalo fada da maganar tsige mataimakin Gwamnan Zamfara

A gefe guda, Punch ta rahoto Sanatan Zamfara ta yamma a majalisar dattawa, Hassan Lawal Dan’iya ya bukaci Bukola Saraki ya rabu da siyasar Zamfara.

Sanata Hassan Lawal Dan’iya ya fadawa tsohon shugaban majalisar dattawa ya guji jefa kansa a abin da ya shafi Zamfara tun da shi ba ‘dan jihar su ba ne.

Hassan Lawal Dan’iya ya fitar da jawabi na musamman, yana mai jan-kunnen Saraki musamman a kan abin da ya shafi tsige mataimakin gwamnan Zamfara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel