Sarakuna 2 sun karfafawa takarar Bola Tinubu, sun bayyana inda ya yi fice a siyasa

Sarakuna 2 sun karfafawa takarar Bola Tinubu, sun bayyana inda ya yi fice a siyasa

  • Sarakunan kasar Kudu maso Yamma sun sa albarka ga shirin neman takarar Bola Tinubu a 2023
  • Asiwaju Bola Tinubu da mutanensa sun ziyarci Sarkin kasar Ife Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi a jiya
  • ‘Dan siyasar ya kuma gana da Lanre Balogun wanda yake jiran a nada shi a kan kujerar Olubadan

Osun - Daya daga cikin kusoshin jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, Asiwaju Bola Tinubu ya kai wa Sarkin kasar Ife Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi ziyara.

Kamar yadda muka samu labari daga shafin Tinubu Support Group a Facebook, Asiwaju Bola Tinubu ya kai ziyara zuwa fadar Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi.

‘Dan siyasar ya gana da Basaraken ne domin ya sa masa albarka a kan neman takarar shugaban kasan da zai yi. Bola Tinubu yace zai nemi shugaban kasa a 2023.

Kara karanta wannan

Mahadi Gusau da jerin Mataimakan Gwamnonin Jihohi 5 da aka canza daga 2015-2022

Mai girma gwamnan jihar Osun, Gboyega Oyetola yana cikin wadanda suka yi wa tsohon gwamnan jihar Legas rakiya zuwa gaban wannan babban Sarki.

Kafin zuwansa kasar Ife, Tinubu ya ziyarci Alaafin na kasar Oyo, Oba Lamidi Adeyemi da kuma Lanre Balogun wanda zai hau karagar sarautar Olubadan a Ibadan.

Tinubu da Alaafin Hoto: pmnewsnigeria.com
Tinubu da Alaafin Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An yabi Bola Tinubu

Jaridar Vanguard ta fitar da rahoto a ranar Alhamis cewa Adeyeye Ogunwusi da Mai martaba Owa Obokun watau Adekunle Aromolaran duk sun yabawa Tinubu.

Oba Adekunle Aromolaran da takwaran na sa sun yabi ‘dan siyasar ne a lokacin da ya kawo ziyara zuwa fadarsu, inda aka ji sun kira shi da mutum na musamman.

Sarakunan sun bayyana Bola Tinubu a matsayin ‘dan siyasar da bai da sa’a wajen gano duk inda wasu ‘yan baiwa suke domin ya ba su matsayi da za su rike masa.

Kara karanta wannan

2023: Jerin gwamnonin da suka ayyana goyon bayansu ga shugabancin Tinubu a bainar jama’a

Mai martaba Ooni ya yi wa Tinubu addu’a domin ya cinma burinsa, ya na mai nuna cewa yana goyon bayansa wajen ganin ya jagoranci Najeriya a zabe mai zuwa.

Da yake bayani a fadar Sarkin Ife da na Mai martaba Obokun, Tinubu ya ce Najeriya ta na da arziki, abin da ya rage shi ne a samu shugaba na gari a kan mulki.

Rikicin APC a Anambra

Kun samu rahoto cewa abubuwa su na kara turnukewa jam’iyyar APC a reshen jihar Anambra yayin da ake shirin gudanar da zaben shugabanni a watan gobe.

Shugabannin jam’iyya da suka kai kara a kotu sun samu nasara, Alkali ya ce uwar jam'yya ta sauke su daga kujerunsu, alhali wa’adin na su bai kare ba tukuna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel