'Sumul kalau nake' Tinubu ya roki yan Najeriya su taimaka su zabe shi a 2023

'Sumul kalau nake' Tinubu ya roki yan Najeriya su taimaka su zabe shi a 2023

  • Bola Tinubu ya ce shugabancin Najeriya na bukatar mutum mai kwakwalwa kuma yana da duk abinda ake bukata
  • Jagoran APC na ƙasa ya tabbatarwa yan Najeriya cewa lafiyarsa kalau, kuma basira ke mulki ba wai kafa ba
  • Ya ce aiki kawai akai masa a kafa, amma yana da manufa mai kyau, kuma yana kaunar ƙasa Najeriya

Osun - Jagoran jam'iyyar APC na ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ce yana da duk wata kwarewa da ake bukata na zama shugaban ƙasa na gaba a Najeriya.

Tinubu ya yi wannan jawabi ne yayin da ya ziyarci Fadar mai martaba Sarkin Osogbo, jihar Osun, ranar Jumu'a, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

'Bola Tinubu
'Sumul kalau nake' Tinubu ya roki yan Najeriya su taimaka su zabe shi a 2023 Hoto: Oluomo Akanbi Ade Afonja/facebook
Asali: Facebook

Ya jaddada cewa ba zai baiwa yan Najeriya kunya ba matukar aka miƙa masa ragamar jagorancin kasar nan, domin kwanya ke aiki ba ƙafa ba.

Kara karanta wannan

2023: El-Rufai ya magantu kan kudirin takarar shugaban kasa, ya bayyana wanda zai marawa baya

Bola Tinubu ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ba aikin Burkila na nema ba, aikin da nake nema na bukatar kwanya. Lafiya ta kalau, ba na cikin rashin lafiya, kawai an ɗan gyara mun guiwata ne."
"Ina da kwarewar yi wa Najeriya aiki, ina son yi wa ƙasa ta aiki kuma ina da kwakwalwa."

Meya kai Tinubu wurin sarakunan?

Tinubu, bisa rakiyar gwamnan Osun, Adegboyega Oyetola, ya fara ziyartar mai martaba Sarkin Ife a Ille Ife, da kuma Sarkin kasar Ijesa a Ilela.

Vanguard ta rahoto ya ce:

"Na zo nan ne domin neman albarkar ku, kuma na zo nan domin neman goyon baya da haɗin kai. Kun san manufa ta kuma kunsan abin da zan iya, dan haka ina bukatar addu'a."
"Na jima ina goyon bayan mutanen nan da kuma can. Mun yawata kowane sashi na ƙasar nan musamman a 2015, lokacin da muka yi yaƙin neman zaben shugaba Buhari."

Kara karanta wannan

Tsohon Mai ba APC shawara ya cire Tinubu, Osinbajo daga lissafin 2023 saboda abu 2

"Ina da manufa kuma na shirya, na shirya zama shugaban ƙasa. Allah da ya dora Sarakunan mu a matsayin da suke, ba zai bar mu ba. Zai taimaka mana. Ina son zama shugaban ƙasa. addu'arku nake bukata."

A wani labarin kuma Gwamnan Kaduna yace kamata ya yi a baiwa mazauna Legas damar shiga Aljanna kyauta saboda wahalar Cunkoso

Gwamna Nasiru El-Rufa'i na jihar Kaduna ya ce wahalar da mutanen Legas ke sha wajen cunkoson ababen hawa na ba shi mamaki.

Gwamnan yace mutanen da suka rayu har tsawon shekar 20 a irin wannan yanayin lallai sun cancanci shiga Aljanna kyauta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel