Emefiele 2023: Kusoshin APC sun dage, su na so Gwamnan CBN ya nemi Shugaban kasa

Emefiele 2023: Kusoshin APC sun dage, su na so Gwamnan CBN ya nemi Shugaban kasa

  • Akwai alamun da ke nuna cewa ana zuga Mista Godwin Emefiele ya tsaya takarar shugaban kasa
  • Masu hannu wajen ganin Gwamnan na bankin CBN ya tsaya takara sun hada da jiga-jigai a APC
  • Ana ganin Shugaban kasa ya yarda da Emefiele, kuma ya yi na’am da tsare-tsaren da ya kawo a CBN

Abuja - Ana ta kokari wajen ganin an shigar da gwamnan bankin CBN, Godwin Emefiele cikin masu neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC.

Jaridar Daily Trust ta ce masu wannan kokari sun hada da manyan kusoshin jam’iyyar APC mai mulki da kuma wasu jami’ai a fadar shugaban Najeriya.

Rahotanni daga majiyoyi masu karfi sun bayyana cewa masu wannan nufin sun hada da wasu gwamnoni na jam’iyyar APC da wasu a fadar Aso Villa.

Kara karanta wannan

Gwamna Tambuwal ya dage domin samun tikitin 2023, ya yi kus-kus da kusan PDP a Arewa

Masu rike da madafan iko sun kawo shawarar a tsaida Emefiele ne saboda ganin yadda gwamnan bankin ya samu shiga a wajen shugaban kasa.

Meyasa ake sha'awar Emefiele?

Wata majiya daga Arewa ta ce akwai manyan Attajiran da ke goyon-bayan Emefiele saboda ganin yadda ya shigo da tsare-tsare domin ba ‘yan kasuwa tallafi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Akwai masu ganin tun da Muhammadu Buhari ya cigaba da aiki da Emefiele duk da gwamnatin Goodluck Jonathan ta nada shi, ya nuna ya san kan aikinsa.

Gwamnan CBN da Shugaban kasa
Shugaban kasa tare da Gwamnan bankin CBN, Godwin Emefiele Hoto: tribuneonlineng.com
Asali: UGC

Jaridar ta ce an fara wannan lissafi ne tun lokacin da Atiku Bagudu ya jagoranci gwamnonin APC suka ziyarci Daura domin taya shugaban kasa murnar sallah.

Kungiyoyi sun fara kiraye-kiraye

Jaridar Vanguard ta ce kungiyoyi irinsu The Green Alliance (TGA) sun fara yin kira ga Emefiele ya amsa masu, ya nemi takarar shugaban kasa a zaben na 2023.

Kara karanta wannan

Jonathan: Asalin abin da ya sa na kirkiro makarantun Almajirai a Arewa a mulkina

Shugaban tafiyar TGA na kasa, Wale Fapohunda ya yi jawabi a wajen wani taro a Legas, ya ce kungiyoyi dabam-dabam su na neman irin Emefiele su tsaya takara.

Fapohunda ya yabi Emefiele a kan manufofin da ya kawo a CBN wanda suka taimakawa dubannan mutane wajen samun aiki, ya kuma karfafa harkar noma.

Wakilan kungiyoyin mata na Asaba Women Association of Nigeria da Women in Politics sun bi bayan TGA, suka ce ya kamata gwamnan CBN ya amsa kiransu.

Zaben fitar da gwani

Idan Godwin Emefiele ya karbi wannan shawara, zai gwabza da su Bola Ahmed Tinubu, Rochas Okorocha, da Orji Uzor Kalu wajen samun tikiti a jam’iyyar APC.

Wadannan mutane duk za su nemi tutar APC a zaben 2023. A gefe guda kuma, an ji akwai rade-radin cewa su Cif Olusegun Obasanjo sun watsar da Atiku Abubakar.

Kara karanta wannan

Shugaban NNPC ya bayyana wadanda suka shigo da rubabben fetur daga kasar waje

Asali: Legit.ng

Online view pixel