2023: Masu neman takara 33 ke zawarcin tikitin gwamna na APC a wata jihar arewa

2023: Masu neman takara 33 ke zawarcin tikitin gwamna na APC a wata jihar arewa

  • Gabannin babban zaben 2023, masu neman takara 33 sun nuna ra'ayinsu na son mallakar tikitin gwamna karkashin APC
  • Shugaban jam'iyyar a Benue, Austin Agada, ya ce akwai karin mutane da za su nuna ra'ayinsu kan kujerar a kwanaki masu zuwa
  • Ya kuma ce tuni sabbin shugabannin da aka rantsar suka kama aiki don ganin sun kwace kujerar gwamnan jihar a 2023

Benue - Akalla masu neman takara 33 ne suka nuna ra’ayinsu na son mallakar tikitin gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Benue.

Shugaban APC a jihar, Kwamrad Austin Agada, ya bayyana a Makurdi a ranar Laraba, 23 ga watan Fabrairu, cewa karin masu neman takara za su ayyana aniyarsu a kwanaki masu zuwa, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kwankwaso, tsohon ministan Buhari: Jerin yan siyasar da suka kafa sabuwar kungiyar siyasa

2023: Yan takara 33 ke zawarcin tikitin gwamna na APC a jihar Benue
2023: Yan takara 33 ke zawarcin tikitin gwamna na APC a jihar Benue Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Agada ya ce:

“A yanzu muna da mutane 33 da suka nuna ra’ayinsu a kan tikitin gwamna karkashin inuwar APC. Akwai karin mutanen da za su nema a nan gaba.”

Agada ya kuma bayyana cewa za a ba dukkanin masu neman takarar filin fafatawa domin su gwada sa’arsu da shahararsu a cikin mutane.

Shugaban jam’iyyar ya kara da cewar sabbin shugabanni da aka rantsar sun dade da fara aiki ba ji ba gani domin ganin APC ta dare kujerar gwamna a babban zaben 2023.

Kwamishinan gwamnan APC ya fice daga jam'iyya, ya koma PDP

A wani labarin, kwamishinan harkokin waje na jihar Imo da ya sauka, Fabian Ihekweme, ya fice daga jam'iyyar APC ya koma PDP mai hamayya.

Kara karanta wannan

Matasan APC a arewa sun bayyana wanda suke so ya gaji Buhari daga kudu maso gabas

Vanguard ta rahoto cewa an gudanar da bikin sauya shekan a filin Nwankwo, Owerri babban birnin jihar, ranar Laraba 23 ga watan Fabrairu 2022.

Shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Dakta Iyorchia Ayu, shi ne ya jagoranci jiga-jigan PDP na ƙasa zuwa taron tarban masu sauya shekan, wanda PDP ta shirya a Owerri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel