Da Dumi-Dumi: Kwamishinan gwamnan APC ya fice daga jam'iyya, ya koma PDP

Da Dumi-Dumi: Kwamishinan gwamnan APC ya fice daga jam'iyya, ya koma PDP

  • Kwamishinan harkokin waje na jihar Imo da APC ke mulki, Fabian Ihekweme, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP mai hamayya
  • Fitaccen ɗan siyasan ya jagoranci dandazon masoya da magoya bayansa a APC zuwa sabuwar jam'iyyar da ya koma PDP
  • Shugaban PDP na ƙasa da Sakatarensa sun yi tattaki har zuwa jahar Imo, domin bikin tarban manyan kusoshin siyasar a Najeriya

Imo - Kwamishinan harkokin waje na jihar Imo da ya sauka, Fabian Ihekweme, ya fice daga jam'iyyar APC ya koma PDP mai hamayya.

Vanguard ta rahoto cewa an gudanar da bikin sauya shekan a filin Nwankwo, Owerri babban birnin jihar, ranar Laraba 23 ga watan Fabrairu 2022.

Shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Dakta Iyorchia Ayu, shi ne ya jagoranci jiga-jigan PDP na ƙasa zuwa taron tarban masu sauya shekan, wanda PDP ta shirya a Owerri.

Wurin taron karban masu sauya sheka a Imo
Da Dumi-Dumi: Kwamishinan gwamnan APC ya fice daga jam'iyya, ya koma PDP Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Daga cikin yan tawagarsa da suka halarci taron, har da Sakataren PDP na ƙasa, Samdaddy Anyanwu, da sauran shugabannin PDP reshen jihar Imo dake kudancin Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shin Kwamishinan ne kaɗai ya koma PDP a wurin taron?

Rahoton da muka samu ya nuna cewa Mista Fabian Ihekweme, ya sauya sheka zuwa bangaren hamayya PDP tare da ɗumbin masoya da magoya bayansa.

Hakanan a wurin taron, shugabannin jam'iyyar sun tarbi wani babban jigo mai faɗa a ji, kuma tsohon shugaban PDP na jihar, Misat Charles Ezekwem.

Ezekwem, fitaccen ɗan siyasa ne a jihar Imo, ya yi watsi da APC mai mulki ya sake rungumar tsohuwar jam'iyyarsa tare da ɗandanzon magoya bayansa, kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.

A wani labarin kuma mun kawo muku Muhimman abubuwa hudu da ya kamata ku sani game da mataimakin gwamna Mahdi Aliyu da Majalisa ta tsige a Zamfara

A yau Laraba, 23 ga watan Fabrairu, 2022, majalisar dokokin jihar Zamfara ta tsige mataimakin gwamna, Barista Mahdi Aliyu Gusau.

Tun bayan sauya shekar gwamna Matawalle daga PDP zuwa APC, alaƙa tai tsami tsakanin su, mun tattaro muku abu hudu game da Gusau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel