Da Dumi-Dumi: Majalisar Dokoki ta tsige mataimakin kakaki, yan majalisu biyu sun sauya sheka zuwa APC

Da Dumi-Dumi: Majalisar Dokoki ta tsige mataimakin kakaki, yan majalisu biyu sun sauya sheka zuwa APC

  • Majalisar dokokin jihar Ebonyi ta bayyana murabus ɗin mataimakin kakaki da wasu mambobinta biyu a zaman Litinin
  • Sai dai lamarin ya tada hatsaniya, yayin da mutanen uku baki ɗaya suka musanta ikirarin majalisa, suna nan daram a matsayin su
  • Rikicin siyasa na cigaba da ƙamari a majalisar dokokin jihar tun bayan sauya shekar gwamnan Dave Umahi

Ebonyi - Majalisar dokokin jihar Ebonyi, a ranar Litinin, ta bayyana kujerar mataimakin kakaki, Odefa Obasi Odefa, a matsayin ba kowa bisa zargin ya yi murabus, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Kazalika mambobin biyu a majalisar, Oliver Osi, mai wakiltar mazaɓar Ivo da kuma Ngozi Ezilo, mai wakiltar Afikpo North East, sun sauya sheka daga PDP zuwa APC.

A cewar kakakin majalisar bayan karanta wasikar mutanen biyu, sun kuma yi murabus daga kasancewarsu mambobin majalisar dokokin jihar Ebonyi.

Kara karanta wannan

Mulki ba naku bane: Obasanjo ya shawarci tsoffin da ke neman tsayawa takara a 2023

Majalisar dokokin jihar Ebonyi
Da Dumi-Dumi: Majalisar Dokoki ta tsige mataimakin kakaki, yan majalisu biyu sun sauya sheka zuwa APC Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Shin menene gaskiyar lamari?

A martanin waɗan da abun ya shafa, Mataimakin shugaban majalisa ya jaddada cewa har yanzun shi ne mataimakin shugaban majalisa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

"Sabida me zan yi murabus? Wannan wasan yara ne. Ban halarci dukkan taron APC ba kuma ban yi murabus ba. Ni ba ɗan jam'iyyar APC bane."
"Idan kana wakiltar mutane, ba kai kaɗai zaka yanke hukunci ba, majalisa ta fahimci ba ta da 2 cikin uku da zata tsige ni, shine ta ayyana cewa na yi murabus. Sabida me zan yi murabus?"
"Shin INEC ta ba wani mamba takardar shaida? Lamarin doka ne yanzu. Sun yi shirin ganin baya na kuma ba zasu iya ba domin ba su suka halicce ni ba. Na zaɓi zama a PDP."

Me sauran yan majalisun biyu suka faɗa kan lamarin?

Kazalika sauran yan majalsu biyu da lamarin ya shafa sun musanta ikirarin majalisa na murabus daga PDP da kuma majalisa baki ɗaya.

Kara karanta wannan

An tsaurara tsaro: Majalisar jiha na shirin tsige mataimakin kakaki bisa kin jinin APC

Honirabul Osi ya ce:

"Mafarki na yi da tsakar rana cewa na yi murabus? Sun hana ni hakkina, motar aiki na da hakkin mazaɓata baki daya sun rike mun."
"Idan da na fice daga PDP ni zan karanta da kaina a zaure, domin za'a kaɗa kuri'ar ra'ayin mambobi kan haka. Wannan hauka ce tuburan."

Yayin zaman, Majaisa ta zabi Mr Kingsley Ikoro, a matsayin sabon mataimakin kakakin majalisar jahar Ebonyi, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

A wani labarin kuma yan awanni bayan sanar da dage taron, Jam'iyyar APC ta sake sanya ranar babban gangamin taronta na kasa

Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta zaɓi ranar 26 ga watan Maris a matsayin ranar babban gangamin taronta na ƙasa.

Sakataren APC na ƙasa, Sanata John James Akpanudoedehe, ya ce za'a fara ayyukan babban taron tun ranar 24 ga watan Fabrairu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel