Bayan kwana 2 da sakinsa, Mu'az Magaji ya ziyarci Shekarau, ya ce gwagwarmaya yanzu suka fara

Bayan kwana 2 da sakinsa, Mu'az Magaji ya ziyarci Shekarau, ya ce gwagwarmaya yanzu suka fara

  • Bayan kwana biyu da sakin Injiniya Mu'azu Magaji, tsohon kwamishinan Ganduje ya ziyarci Sanata Ibrahim Shekarau a gidansa da ke Kano
  • Kamar yadda Dan Sarauniya ya sanar da manema labarai, ya ce wannan abu da ya faru da shi karin karfin guiwa ne na gwagwarmaya
  • Ya bayyana cewa, biyayyarsa ta koma ga tsagin Shekarau tunda ya gano cewa su ke da nufi nagari ga Kanawa da siyasar kasar nan

Kano - Kwanaki biyu bayan bada belin tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Kano, Muazu Magaji, wanda ya kasance a gidan yari kan zargin batawa gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje suna, ya bayyana goyon bayansa ga tsagin Sanata Ibrahim Shekarau.

A wata ziyara ta musamman ga shugaban tsagin jam'iyya mai mulkin a gidan Sanata Shekarau, Magaji ya gana da Sha'aban Sharada, Danzago da wasu jiga-jigan jam'iyyar, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kano: Kotu ta sake bayar da belin korarren kwamishinan Ganduje, Ɗan Sarauniya

Bayan kwana 2 da sakinsa, Mu'az Magaji ya ziyarci Shekarau, ya ce gwagwamaya yanzu suka fara
Bayan kwana 2 da sakinsa, Mu'az Magaji ya ziyarci Shekarau, ya ce gwagwamaya yanzu suka fara. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, Sai dai kuma, a wata tattaunawar gaggawa da manema labarai a gidan Shekarau a ranar Lahadi, Injiniya Magaji ya ce biyayyarsa yanzu ta koma wurin tsagin Shekarau saboda su ne suke yi wa Kano fatan alheri.

"Allah ya kawo mu nan a tafiyar siyasar mu wanda a kowanne tarihi za mu ce kara mana karfin guiwa yayi wurin gwagwarmaya. Mun je kotu kuma alkali ya bayar da belin mu da sharadin mu gujewa yin tsokaci kan lamarin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Za mu yi biyayya ga hukuncin kotun saboda mu 'yan kasa ne masu bin dokoki. Muna tsagi daya da shugabanmu Shekarau saboda mun gane cewa sun dauka sabon salo wanda ya kai ga suna rike da ragamar jam'iyya a Kano a shari'ance da kuma siyasance.
"Za mu cigaba da rajin ganin an yi abinda ya dace, fadin gaskiya da kuma tsayuwa kan gaskiya. Abinda za mu yi nan gaba shi ne karfafa kungiyar mu wurin samun nasarar kafa sabuwar Kano kamar yadda muka zo samun albarkar shugabanmu.

Kara karanta wannan

Kisan Hanifa Kano: Matan Arewa sun bukaci gwamnati ta hukunta iyaye saboda abu ɗaya

“Burinmu a yanzu shine tattaro matasan Kano da kasar nan baki daya wurin samar da dama da za ta sauya tsarin shugabanci.
"Babu shakka akwai sadaukarwa kuma dole sai an fuskanci kalubale yayin sadaukarwa. Babu kuma raguwa idan har za ka tabbatar da cewa an yi komai daidai."

Kano: Kotu ta sake bayar da belin korarren kwamishinan Ganduje, Ɗan Sarauniya

A wani labari na daban, wata kotun majistare mai lamba 58 karkashin alkalanci Aminu Gabari ta sake bayar da belin tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Kano, Mu'azu Magaji wanda aka fi sani da Dan Sarauniya.

Lauyan wanda ake zargi, Garzali Datti Ahmed, ya mika bukatar sake duba sharuddan belin inda ya yi kira ga kotun da ta duba bukatarsa.

A hukuncin kotun wanda ta bayar da belin Magaji a ranar 4 ga watan Fabrairu, ta saka wasu sharuddan da za a cika kafin karbarsa, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Jagoran Win/Win Mu'az Magaji ya nemi a sassauta masa sharuɗan belin da aka sanya masa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel