Kano: Kotu ta sake bayar da belin korarren kwamishinan Ganduje, Ɗan Sarauniya

Kano: Kotu ta sake bayar da belin korarren kwamishinan Ganduje, Ɗan Sarauniya

  • Alkali Aminu Gabari na kotun majistare mai lamba 58 ya sake bayar da belin tsohon kwamishinan ayyuka, Mu'azu Magaji
  • A halin yanzu, kotun ta amince da babban limamin Dan Sarauniya ya tsaya wurin fito da Mu'azu Magaji
  • Sai dai kotun ta bukaci ya guje wa duk wata wallafa daga soshiyal midiya har sai an kammala shari'ar kuma ya biya gilashin motar gidan yari da magoya bayansa suka fasa

Kano - Wata kotun majistare mai lamba 58 karkashin alkalanci Aminu Gabari ta sake bayar da belin tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Kano, Mu'azu Magaji wanda aka fi sani da Dan Sarauniya.

Lauyan wanda ake zargi, Garzali Datti Ahmed, ya mika bukatar sake duba sharuddan belin inda ya yi kira ga kotun da ta duba bukatarsa.

Kara karanta wannan

Dirama ta ɓarke a Kotu yayin da Amarya ta yi ikirarin Ango ya danna mata saki uku a waya

A hukuncin kotun wanda ta bayar da belin Magaji a ranar 4 ga watan Fabrairu, ta saka wasu sharuddan da za a cika kafin karbarsa, Daily Trust ta ruwaito.

Kotun ta bada belinsa kan kudi har N1 miliyan da tsayayyu biyu wadanda za su kasance dagacin kauyen Dan sarauniya, kwamandan Hisbah daga Dawakin Tofa ko kuma babban limami.

Kano: Kotu ta sake bayar da belin korarren kwamishinan Ganduje, Ɗan Sarauniya
Kano: Kotu ta sake bayar da belin korarren kwamishinan Ganduje, Ɗan Sarauniya. Hoto daga dailytrust.com
Asali: Facebook

Sai dai kuma, takardun kotun da lauyan Magaji ya samu sun bayyana cewa alkalin ya sanar da lauyan daga baya cewa ya na nufin babban limamin Dawakin Tofa nufi ba na kauyen Dan Sarauniya ba.

Sai dai a takardar da Hamza Shariff ya fitar, sakataren kara na bangaren lauyan Magaji, ya sanar da kotun cewa sharuddan sun yi tsauri balle kuma batun kawo babban limamin Dawakin Tofa.

Kara karanta wannan

Sokoto: Kansila ya gwangwaje 'yan unguwarsa da kyautar tabarmai 2, ya jawo cece-kuce

Ta ce"

"Babban limamin Dawakin Tofa karkashin Dagacin Dawakin Tofa Isma'ila Umar Ganduje ya ke, kuma dagacin dan uwan mai korafin ne, uwa daya, uba daya."

Takardun kotun sun kara bayyana cewa, bayan an tuntubi babban limamin Dawakin Tofa domin ya tsaya wa Magaji, ya ce ba zai iya ba saboda umarni daga dagacinsa ya ke iya karba.

An sanar da kotun cewa, dukkan manyan limaman yankin sun ce ba za su iya tsayawa Magaji ba illa babban limamin kauyen Dan Sarauniya.

A yammacin Juma'a, kotun ta amsa bukatar lauyan Magaji inda ta sake duba sharuddan belin tare da amincewa da babban limamin kauyen Dan Sarauniya a maimakon na Dawakin Tofa.

Sai dai, alkalin ya hana Magaji cigaba da wata wallafa a soshiyal midiya har sai an kammala sharia'a, Daily Trust ta ruwaito.

Alkalin ya bukaci Magaji da ya biya gilashin motar gidan gyaran halin da magoya bayansa suka fasa, wanda Datti Ahmed ya ce za su duba hakan domin ba su da labarin.

Kara karanta wannan

Jagoran Win/Win Mu'az Magaji ya nemi a sassauta masa sharuɗan belin da aka sanya masa.

An dage sauraron shari'ar zuwa ranar 2 ga watan Maris mai zuwa.

Dan Sarauniya ya kurmance a kotu, ya tilasta Alkali dage zama

A wani labari na daban, tsohon kwamishanan ayyuka na jihar Kano, Muaz Magaji, wanda aka fi sani da 'Dan Sarauniya' ya kurmance a cikin kotu yayinda ake shirin gurfanar da shi ranar Juma'a.

A cewarsa, hakan ya faru sakamakon wani hadarin ya samu lokacin da yan sanda ke binsa a Abuja ranar Alhamis, rahoton DailyNigerian.

An damke Muazu Magaji ne ranar Alhamis a Abuja yayinda yake kokarin gudunma yan sandan dake binsa kuma yayi hadari sakamakon haka.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel