Rikicin APC a Kano: An kammala shirya komai domin yin sulhu, Ganduje

Rikicin APC a Kano: An kammala shirya komai domin yin sulhu, Ganduje

  • Shugaban kwamitin kula ta hadin gwiwa na kasa da kuma jihohi na jam’iyyar APC, da gwamnan Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, sun ce kwamitin ta gama shirya taron sasancin jihar
  • Kwamishinan labarai, Malam Muhammad Garba, ya saki wata takarda wacce ya tabbatar da cewa har an samar da wurin da za a yi taron wanda za a fara ranar Juma’a, 11 ga watan Fabrairun 2022 a birnin Kano
  • Gwamnan ya tabbatar wa jiga-jigan jam’iyyar APC na kasa da jihar cewa a shirye kwamitin take da ta kawo hadin-kai da ci gaban jam’iyyar a cikin jihar da kasar baki daya

Kano - Shugaban kwamitin kula ta hadin-gwiwa na kasa da jihohi na jam’iyyar APC da gwamnan Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, sun ce kwamitin ta gama duk wasu shirye-shiryen da suka dace na hada kai da sauran mambobin kwamitin don zama teburin sasanci a jihar, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: Manyan jiga-jigan PDP a Jigawa sun marawa dan Lamido baya don samun tikitin gwamna na jam’iyyar

Rikicin APC a Kano: An kammala shirya komai domin yin sulhu, Ganduje
APC: Gwamna Ganduje na Kano ya ce an kammala shirya komai domin yin sulhu a jihar. Hoto: Vanguard
Source: Twitter

Wata takarda wacce kwamishinan labarai na jihar, Muhammad Garba ya saki ta yanko daidai inda Gwamna Ganduje ya ce an samar da wurin da za a yi taron wanda za a fara a ranar Juma’a, 11 ga watan Fabrairun 2022 a babban birnin jihar.

Kamar yadda takardar ta nuna:

“Ganduje ya tabbatar wa mambobin jam’iyyar APC da jiga-jiganta na jihar cewa mambobin kwamitin a shirye suke da su samar da hadin-kai da ci gaban jam’iyyar da ma kasa baki daya.”

Akwai masu fadi a ji na jam’iyyar a cikin kwamitin

Kwamitin wacce babban ofishin jam’iyyar na kasa ya shirya tana da mambobi kamar Sardaunan Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, Gwamna Bello Matawalle, Hon. Yakub Dogara da Sanata Abba Ali.

An ba kwamitin kwana bakwai don ta kawo rahoto kamar yadda Vanguard ta bayyana.

Kara karanta wannan

Guguwar sauya sheka: Ana gab da yiwa APC mai kankat gabannin 2023 - Tambuwal

Sai dai wata kungiya mai suna APC “Masalaha”, wacce ta kunshi manyan shugabannin APC na Kano, ciki har da Hon. Yusuf Ado Kibiya a matsayin Shugaba, Kabiru Kamakasa, a matsayin darektan tsare-tsare, Hamisu Lamido Iyantama a matsayin darektan watsa labarai da kuma Farfesa Mukhtar A Yusuf a matsayin sakatare janar sun bukaci a nemi zaman lafiya, adalci, daidaito da kuma dabarun demokradiyya don kawo karshen rikicin jam’iyyar na jihar.

APC Masalaha ta ce rikicin zai iya shafar zaben 2023 na kasa baki daya da ke karatowa

A wata takarda wacce manyan APC din suka sakar wa manema labarai a Kano ranar Alhamis, APC Masalaha ta bukaci a yi zama na lumana don kawo karshen rikicin nan mara kyau da ba a bukata.

Kamar yadda wani bangare na takardar ya zo:

“A ganin mu wajibi ne bangarorin masu fada da juna su girmama burika da ra’ayin juna.
“A dayan bangaren kuma, babban ofishin jam’iyya na kasa ya samar da mafita ga APC din Jihar Kano saboda hakan zai iya taba gaba daya zaben da za a yi a kasa.
“Ta yi kokarin hada kawunan su don samar da alaka mai kyau da kuma ganin rikicin bai maimaita kan sa ba.”

Buhari: Na Ji Daɗin Yadda Masu Hannu Da Shuni Suka Gane Cewa Canja Najeriya Ba Aikin Mutum Ɗaya Bane

Kara karanta wannan

Gwamnoni, Sanatoci, tsofaffin masu mulki 100 sun hadu domin ceto Najeriya kafin zaben baɗi

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ya yi farin cikin sanin cewa kusoshin Najeriya sun gane cewa canja kasar nan aikin kowa ne, The Cable ta ruwaito.

Kamar yadda kakakin shugaban kasa, Femi Adesina ya bayyana a wata takarda, Buhari ya yi wannan furucin ne a ranar Lahadi a wata liyafa ta girmama shugabannin kwamitin kasuwanci, siyasa, kafafen watsa labarai da sauran ma’aikata.

Dama a watan Janairun 2021 The Cable ta bayyana yadda Buhari ya zargi masu fada a jin kasar nan da kawo cikas ga gwamnatin sa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164