Gwamnan Jigawa: Ka'idojin da magajin kujera ta zai cika a zaben 2023

Gwamnan Jigawa: Ka'idojin da magajin kujera ta zai cika a zaben 2023

  • Gwamna Muhammad Badaru Abubakar na jihar Jigawa ya magantu a kan wanda ya cancanci ya gaje shi a zaben 2023
  • Badaru ya ce ya zama dole duk wanda zai dare kujerar gwamnan jihar ya zamo mutum mai tawali’u, rashin son kai da kuma sauraron jama'a
  • Ya bayyana hakan ne bayan ya amsa gayyatar wata kungiya mai zaman kanta ta Hadejia Ina Mafita

Jigawa - Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, ya bayyana cewa mutum mai tawali’u da rashin son kai ne ya fi cancanta ya gaje shi a zaben 2023.

Badaru ya bayyana hakan ne bayan ya amsa gayyatar wata kungiya mai zaman kanta ta Hadejia Ina Mafita, a ranar Litinin, 7 ga watan Fabrairu, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Ya kamata PDP ta karɓe mulkin Najeriya, zaman lafiya ya gagara, inji gwamnan PDP

Gwamnan Jigawa: Ka'idojin da magajin kujera ta zai cika a zaben 2023
Gwamnan Jigawa: Ka'idojin da magajin kujera ta zai cika a zaben 2023 Hoto: Daily Trust
Source: Facebook

Gwamnan na gab da kammala wa’adin mulkinsa, domin ya zama gwamnan jihar Jigawa ne a 2015 sannan aka sake zabarsa a 2019.

Da yake bayyana cewa hakkin mutanen jihar Jigawa ne su yanke shawara kan wanda suke so ya zama gwamnansu a 2023, gwamnan ya ce ya zama dole wanda zai gaje shi ya zama mutum mai sauraron mutanen jihar.

Daily Trust ta rahoto Badaru yana cewa:

“Addu’a na shine cewa mu samu mutum mai tawali’u, mai tsoron Allah kuma wanda zai ci gaba daga inda muka tsaya kuma wanda zai saurari mutane kamar yadda muke yi.
“Fatana shine cewa dole gwamna nagaba ya zama mutum mai adalci, mai sauraron mutane.”

Bayan shekaru 49, shahararren mai neman shugabancin kasa na PDP ya ziyarci garinsu da sunan zai tsaya takara

Kara karanta wannan

Bayan shekaru 49, shahararren mai neman shugabancin kasa na PDP ya ziyarci garinsu da sunan zai tsaya takara

A wani labari na daban, jigon jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Cif Dele Momodu, ya ziyarci mahaifarsa ta Ihevbe a karamar hukumar Owan East ta jihar Edo domin ayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa, a ranar Lahadi, 7 ga watan Fabrairu.

Momodu ya dage cewa lallai shine ya fi cancanta a tsakanin wadanda ke neman darewa kujerar shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar 29 ga watan Mayun 2023, jaridar The Nation ta rahoto.

Dan siyasar ya samu tarba daga daruruwan mutanen Ihevbe yayin da ya ce ya daura aniyar neman shugabancinsa ne daga ganin cewar koda dai ba a taba zabarsa wani mukami ba, ya zauna a gujera daya da manyan mutane a fadin duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng