Sabuwar Matsala: Ɗaruruwan mambobin PDP a jihar da take mulki, sun sauya sheƙa zuwa APC

Sabuwar Matsala: Ɗaruruwan mambobin PDP a jihar da take mulki, sun sauya sheƙa zuwa APC

  • Jam'iyyar PDP mai mulki a jihar Edo ta gamu da cikas, yayin da ɗaruwawan mambobinta suka koma APC a mazaɓar Ovia
  • Masu sauya sheƙan sun bayyana cewa sun ɗauki matakin ne saboda ayyukan raya ƙasa da ɗan majalisa mai wakiltar Ovia a tarayya ke yi
  • Ɗan majalisan, wanda ya karbe su, a halin yanzun sun shigo gida, babu wanda zai nuna musu banbanci

Edo -Ɗaruruwan mambobin jam'iyyar PDP mai mulkin jihar Edo sun sauya sheka zuwa APC, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Sun bayyana cewa sun koma APC ne saboda kwaɗayin kyakkyawan jagorancin da mamba a majalisar wakilan tarayya mai wakiltar Ovia, Hon Dennis Idahosa, ke gudanarwa al'ummarsa.

Karkashin jagorancin Mista Balogun Okhiwere, waɗan da suka sauya sheƙan sun faɗi cewa sun dawo APC ne domin su haɗa ƙarfi da ƙarfe kuma su taimaki ɗan majalisar ya cigaba da ayyuka nagari.

Kara karanta wannan

Sabon Rikici: Jam'iyyar PDP ta dakatar da Surukin gwamnanta da wasu jiga-jigai uku, zasu koma APC

Tutar PDP
Sabuwa Matsala: Ɗaruruwan mambobin PDP a jihar da take mulki, sun sauya sheƙa zuwa APC Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Okhiwere ya jaddada cewa duk yawan waɗanda suka sauya sheƙan suna son runguman gaskiya kuma a yi aiki tare domin ƙara karfi kan wanda suka taras.

Ya ce wasu daga cikin waɗanda suka koma APC ɗin tare da shi, kusoshi ne da suka koma PDP amma yanzun sun dawo gida.

A jawabinsa yace:

"Mu mambobin PDP a mazaɓar Ovia dake arewa ta gabas mun fice daga jam'iyya, mun koma APC domin yaba wa Honorabul Dennis Idahosa bisa dumbin ayyukan raya ƙasa da yake kawo wa mazaɓar mu."

Kun zama cikakkun 'ya'yan APC

Ɗan majalisan wanda ya karɓe su, ya yaba musu bisa ƙarfin guiwar da suke da ita, yace sun zama yan gida, kuma ba za'a nuna musu wariya ba.

Yace:

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Yan bindiga sun kai mummunan hari kan mutanen ƙauye, Sun halaka Manaja da yaronsa

"Kun zama wani sashin mu tun kafin ku shigo kuma ina mai ƙara jaddada muku ba bu wani sabo da tsohon mamba a APC, da mu da ku duk mun zama ɗaya."
"Ina rokon ku yi aiki tukuru kuma cikin haɗin kai domin mu haɗa kai wajen cimma burin mu na haɓaka mazaɓar Ovia."

A wani labarin na daban kuma Gwamnan Arewa ya karɓi tuban dandazon mambobin APC da suka sauya sheka zuwa PDP a jiharsa

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya karbi sabbin mambobin PDP da suka sauya sheka daga APC a fadar gwamnatinsa.

Dandazon mambobin APC sun sauya sheka zuwa PDP a yankin Awalah dake cikin kwaryar birnin Bauchi ranar Lahadi

Asali: Legit.ng

Online view pixel