Jerin Tsofaffin Gwamnoni da Basu Ga Maciji da Yaran Gidansu Bayan Ɗarewa Mulki

Jerin Tsofaffin Gwamnoni da Basu Ga Maciji da Yaran Gidansu Bayan Ɗarewa Mulki

A Najeriya, ana yawan samun matsala tsakanin manyan ƴan siyasa da kuma yaran gidansu da suka tsayar takara.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Mafi yawan wadanda ake tsayarwa daga baya suna yin kunnen uwar shegu ga umarnin iyayen gidansu wanda hakan ke jawo matsala.

Tsofaffin gwamnoni da basu ga maciji da yaran gidansu
A Najeriya ana yawan samun matsala tsakanin tsofaffin gwamnoni da kuma wadanda suka daura mulki. Hoto: Adams Oshiomole, Rabi'u Musa Kwankwaso, Nyesom Wike.
Asali: Facebook

Matsalar da ake samu da tsofaffin gwamnoni

Hakan bai rasa nasaba da neman iko kan lamuran mulkin jiha domin ci gaba da kasancewa a fagen juya akalar jiha.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit Hausa ta jero muku kadan daga cikin jihohin da aka samu matsala tsakanin yaran da iyayen gidansu a siyasa.

1. Kano: Kwankwaso vs Ganduje

Kara karanta wannan

Kungiya ta wanke Ganduje daga zargin rashawa, ta kalubalanci gwamnatin Kano

Tsawon lokaci Rabiu Kwankwaso na ɗasawa da Abdullahi Ganduje a matsayin yaronsa wanda ke ma sa biyayyya.

Ganduje ya yi mataimakin Kwankwaso har sau biyu a 1999 zuwa 2003 da kuma 2011 zuwa 2015 kafin lamura su dagule.

Hawan Ganduje kujerar gwamna a 2015 ke da wuya komai ya tabarbare a tsakaninsu wanda har yanzu ba a damu jituwa ba.

Daga bisani, Shugaba Tinubu ya bukaci a sasanta tsakani wanda hakan bai yi tasiri ba illa kara lalata lamura a tsakaninsu.

Tsagin jam'iyyar APC ya dakatar da Ganduje a matsayin shugaban jam'iyyar wanda ake zargin Kwankwaso da saka hannu a matsalolin da Ganduje ke fuskanta a yanzu.

2. Kaduna: El-Rufai vs Uba Sani

Gwamna Uba Sani da mai gidansa, Nasir El-Rufai sun ci gaba da dasawa bayan tsohon gwamnan ya bar kujerar mulki.

Komai ya rikice ne a tsakaninsu bayan Uba Sani ya zargi El-Rufai da bar masa tulin bashi da ya hana jihar samun kudin shiga.

Kara karanta wannan

Ana kishin kishin, an fara neman wanda zai karbi kujerar APC a hannun Ganduje

Daga bisani, Uba Sani ya kafa kwamitin binciken basuka da badakalar kudi na gwamnatin El-Rufai a jihar Kaduna.

3. Gombe: Goje vs Inuwa

Gwamnan Inuwa Yahaya ya rike mukamin kwamishina a lokacin mulkin Danjuma Goje a jihar Gombe.

Daga bisani, Goje ya marawa Inuwa baya a 2019 inda ya yi nasarar kasancewa gwamnan jihar.

Daga nan ne komai ya rikice inda aka fara takun-saka kowa na son nuna ikonsa na mulki wanda har ya kawo ƴar tsohon gwamnan, Dakta Hussaini Goje ta yi murabus daga mukamin kwamishina.

A daf da zaben 2023, jam'iyyar APC ta kasa ta kira sulhu a tsakaninsu wanda aka samar da maslaha da kuma gudanar da zaben fidda gwani lafiya.

4. Edo: Oshiomole vs Obaseki

Godwin Obaseki wanda yaron Adams Oshiomole ne ya shiga yaki da uban gidansa wanda ya ba shi mukami a lokacin mulkinsa.

Oshiomole ya daga hannun Obaseki a 2016 a jam’iyyar APC kafin komai ya tabarbare cikin kankanin lokaci da kuma komawa jam’iyyar PDP da Obaseki ya yi a kokarin neman zarcewa.

Kara karanta wannan

Ana tsoron rikici kan tukunyar miya ya jawo asarar rayuka a birnin Abuja

Rashin jituwa tsakanin Obaseki da Oshiomhole ne ya sa gwamnan ya bar jam'iyyar APC zuwa PDP.

A yanzu Oshiomhole sanata ne a jihar Edo yayin gwamna Obaseki na PDP ke daf da kammala wa'adinsa a matsayin gwamnan jihar.

5. Rivers: Wike vs Fubara

Alakar Ministan Abuja, Nyesom Wike da yaronsa Gwamna Siminalayi Fubara sai kara lalacewa ta ke yi watanni biyar bayan Wike ya bar mulki.

A kwanakin nan lamarin ya kara zafi duk da kokarin sasantawa da Shugaba Bola Tinubu ya yi.

A cikin wannan mako kadai, kwamishinoni hudu ne suka yi murabus daga gwamnatin Fubara wadanda ke goyon bayan Wike.

Duk da haka Fubara ya sha alwashin take dukkan wanda zai kawo masa barazana a cikin mulkinsa.

Wike ya ba da hakuri kan Fubara

Kun ji cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ba ƴan jihar Rivers hakuri kan zaben Siminalayi Fubara a matsayin magaji.

Kara karanta wannan

Bulaliyar kan hanya: Tinubu, Shettima za su fara biyan harajin fakin a filin jirgin sama

Wike ya bayyana cewa ya tafka babban kuskure kuma zai gyara dukkan kura-kurai da ya yi a baya yayin zaben da za a yi a gaba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel