Hawan Jini: "28.5% na Mutanen Kano na Dauke da Muguwar Cuta" Inji Gwamnati

Hawan Jini: "28.5% na Mutanen Kano na Dauke da Muguwar Cuta" Inji Gwamnati

  • Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa wasu daga al'umarta tsakanin shekara 30-79 na fama da hawan jini
  • Kwamishinan lafiya a jihar, Dr. Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana hakan a bikin ranar kare kamuwa da hawan jini na bana
  • Kwamishinan ya kara da cewa kaso 28.5 a tsakanin shekarun ne ke fama da cutar, kuma akwai yiwuwar fa janyo wasu cututtukan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano- Ma'aikatar lafiya a jihar Kano ta bayyana cewa da kimanin kaso 28.5 na wadanda ke da shekaru 30-79 ne ke fama da ciwon yawan jini.

Da yawa daga cikinsu ba su san da ciwon a jikinsu ba, duk da illar da ya ke tattare da shi, in ji ma'aikatar.

Kara karanta wannan

Kwara: Sun fadi gaskiya bayan cafke likita da wasu da zargin satar mahaifa da cibiyar jariri

Hawan jini
Ana fama da hawa jini a Kano Hoto: Barisonal
Asali: Getty Images

Daily Trust ta wallafa cewa kwamishinan laifa, Dr. Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana hakan yayin taron ranar kare kamuwa da hawan jini na bana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hawan jini na jawo wasu cututtuka

Kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dr. Abubakar Labaran Yusuf ya bayyana cewa yawan jini na tattare da illoli da dama.

Ya shaida haka ne a taron kare kamuwa da ciwon yawan jini na bana mai taken 'a yi gwajin hawan jini, a kula domin samun tsawon rai'.

Dr. Labaran ya ce hawan jini na janyo cututtuka kamar na shanyewar barin jiki, ciwon zuciya da ciwon koda,kamar yadda Arewa Agenda ta wallafa.

Gwamnati za ta taimakawa masu hawan jini

Kwamishinan ya bayyana cewa za a yi gwajin hawan jini kyauta a karamar hukumar Gwale a cikin shirin bikin ranar hana kamuwa da cutar.

Kara karanta wannan

Rivers: Gwamna ya kuma ɗaga yatsa ga Wike, ya bugi kirji kan jikkata abokan gaba

Ya kara da cewa gwamnati za ta rage kudin kula da masu yawan jini a dukkanin asibitocin gwamnatin Kano.

Haka kuma za a kula da kula da masu cutar kyauta ta cikin tsarin taimakekeniyar lafiya ta KSCHMA.

Yan harin masallaci sun kara mutuwa

Mun kawo mu ku labarin cewa adadin wadanda su ka rasu a harin masallaci a jihar Kano ya kai 15, bayan harin da wani matashi Shafi'u Abuabakar ya yi.

Matashin ya kai wa masallata hari ne bisa abun da ya kira kananun magana da su ke fada a kansa, kuma ya musu magana sun ki ji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.