Fayose ya nunawa ‘Yan PDP har yanzu da sauransu, ya fito da ‘Dan takaran Gwamna a Ekiti

Fayose ya nunawa ‘Yan PDP har yanzu da sauransu, ya fito da ‘Dan takaran Gwamna a Ekiti

  • ‘Ya ‘yan jam’iyyar PDP sun fito da ‘dan takarar gwamna a zaben gwamnan jihar Ekiti da za ayi a bana
  • ‘Dan takarar da Ayo Fayose ya tsaida, Bisi Kolawole ne ya yi nasara, zai rike tutar jam'iyyar PDP
  • Hon. Kolawole ya doke manyan ‘yan PDP a jihar Ekiti irinsu tsohon gwamna Oni da Sanata Olujimi

Ekiti - Bisi Kolawole aka zaba a matsayin ‘dan takarar gwamnan jihar Ekiti a karkashin jam’iyyar PDP. The Cable ta fitar da wannan rahoton a ranar Laraba.

Hon. Bisi Kolawole zai kara da sauran wadanda APC da sauran jam’iyyu suka tsaida a zaben gwamnan da za a gudanar a ranar 18 ga watan Yunin 2022.

Bisi Kolawole ya sauka daga kujerar da yake kai na shugaban jam’iyyar PDP, ya shiga zaben fitar da gwanin, ya kuma yi nasarar doke manyan ‘yan siyasa.

Kara karanta wannan

Buhari ya sake zabar yar APC a matsayin kwamishinar INEC, HURIWA ta kai kara majalisa

Kafin zamansa shugaban jam’iyyar hamayya na reshen jihar Ekiti, Kolawole ya taba wakiltar mazabar Efon a majalisar dokoki na Ekiti a karkashin PDP.

Tsakanin 2015 zuwa 2018 a lokacin da Ayo Fayose yake gwamna, Kolawole ya rike kwamishinan muhalli. Fayose ne ya tsaya masa wajen ganin ya samu tikiti.

Ekiti
Hon. Bisi Kolawole da Udom Emmanuel Hoto: @AMTanimu/Twitter
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Fayose ya saki Kolapo Olusola

Legit.ng ta fahimci cewa Kolawole ya doke tsohon gwamna Segun Oni da tsohon ‘dan takarar gwamna a PDP, Kolapo Olusola wajen samun tikitin 2022.

Jaridar ta ce a zaben tsaida ‘dan takara da aka yi wannan karo, tsohon gwamna Fayose ya yi watsi da mataimakinsa, Olusola Kolapo, ya goyi bayan Kolawole.

A zaben 2018, Farfesa Kolapo ya samu goyon bayan mai gidansa kuma gwamna mai-ci a lokacin, Fayose, amma ya sha kashi a hannun Kayode Fayemi na APC.

Kara karanta wannan

Kaduna 2023: Dattijo, Sanata Uba Sani da ‘Yan siyasa 7 da ke harin Gwamna a APC

Sakamakon zaben da aka yi a Ado Ekiti

Kayode Adaramodu - 10

Kazeem Ayodeji - 6

Olusola Kolapo - 93

Deborah Ali - 1

Ojo - 1

Makanjuola - 1

Biodun Olujimi - 2

Aderemi Adewumi - 1

Adewale Aribisala - 56

Segun Oni - 330

Bisi Kolawole - 671

Sai dai duk ta samu kuri'u a zaben tsaida 'dan takarar, Sanata Biodun Olujimi ta ba kwamitin gwamna Udom Emmanuel sanarwar janyewa daga zaben.

Rikicin APC a Kebbi

Ku na da labarin cewa zargin kokarin kakaba Abubakar Malami SAN a matsayin ‘dan takarar gwamna ya jawo matsala a jam'iyyar APC ta reshen jihar Kebbi.

An samu rabuwar kai tsakanin ‘ya ‘yan jam’iyyar APC a jihar Kebbi saboda wannan shirin. Irinsu Adamu Aliero da Yahaya Abdullahi su na fito na fito da gwamna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel