Kaduna 2023: Dattijo, Sanata Uba Sani da ‘Yan siyasa 7 da ke harin Gwamna a APC

Kaduna 2023: Dattijo, Sanata Uba Sani da ‘Yan siyasa 7 da ke harin Gwamna a APC

  • An fara lissafin wanda jam’iyyar APC za ta tsaida takarar Gwamna a jihar Kaduna a zaben 2023
  • Uba Sani, Bashir Sa’idu da Dattijo su na cikin wadanda ake ganin za su gwabza a Jam’iyyar APC
  • Mataimakiyar gwamna, Mai girma Hadiza Sabuwa Balarabe ta shiga cikin jerin da mu ka kawo

Kaduna - A halin yanzu ‘yan siyasa sun fara lissafin zaben 2023 a Najeriya. A karshen wannan shekarar ne za a soma maganar shiga zaben fitar da ‘yan takara.

Jihar Kaduna ta na cikin jihohin da mutane za su ga yadda makomar siyasar za ta kasance a 2023 ko saboda gawurtattun ‘yan siyasarta da yawan mutanenta.

Legit.ng Hausa ta kawo maku jerin wasu daga cikin manyan ‘yan siyasar da ake ganin za su iya neman zaben fitar da gwanin takarar gwamna a jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan

Farin jinin Buhari, da abubuwa 8 da za su taimakawa Osinbajo a takarar Shugaban kasa

Daga cikin wadanda ake gani su na gaba-gaba a wajen neman tikitin a halin yanzu akwai:

1. Hadiza Sabuwa Balarabe

A 2019 Hadiza Sabuwa Balarabe ta kafa tarihin zama mataimakiyar gwamnan Kaduna. Ana ganin tana cikin wadanda za su iya neman tsayawa takarar gwamna a 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wannan kwararriyar likita za ta iya fuskantar kalubale a zabe, daga ciki har da yankin da ta fito.

2. Muhammad Bashir Sa’idu

Masu fashin-bakin siyasar su na ganin Bashir Sa'idu ya na cikin wadanda za a gwabza da su. Kafin zamansa kwamishinan kudi, shi ne shugaban ma’aikatan gidan gwamnati.

Kaduna
Gwamna El-Rufai Hoto: Gov Kaduna / Facebook
Asali: Facebook

3. Balarabe Abbas Lawal

Kamar Bashir Sa’idu, shi Malam Balarabe Abbas Lawal yana cikin masu karfi a gwamnatin El-Rufai. Akwai yiwuwar sakataren gwamnatin ya nemi APC ta ba shi tuta.

4. Uba Sani

Sanatan Kaduna ta tsakiya, Uba Sani ya shiga wannan jerin na mu. Alamu sun nuna tsohon hadimin na Nasir El-Rufai yana cikin wadanda ake yi wa kallon ‘yan gaba-gaba.

Kara karanta wannan

Yadda yunkurin zawarcin Jonathan, a ba shi takara a APC ya sha ruwa tun kafin a kai 2023

5. Muhammad Sani Abdullahi

Malam Muhammad Sani Abdullahi wanda aka fi sani da Dattijo shi ne na karshe a jerin. Ana tunanin tsohon shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin zai nemi gwamna.

Sauran masu sha'awar zama Gwamna

Wata majiya ta shaidawa Legit.ng Hausa cewa shugaban hukumar nan ta NIMASA, Dr. Bashir Yusuf Jamoh ya na cikin wadanda ake yi wa ganin harin gwamna.

Akwai wasu da ake tunanin su na sha’awar neman takara a jam’iyyar APC, daga ciki har da Mohammad Mahmud wanda yanzu Minista ne a gwamnatin Buhari.

Meya faru da Dattijo?

Kwanakin baya aka ji Malam Muhammad Sani Dattijo ya rasa mukaminsa a wani sauyi da Gwamna El-Rufai ya yi a gwamnatinsa wanda ya ba mutane mamaki.

Nasir El-Rufai ya bada sanarwar sauke Dattijo daga kujerar da yake kai ta shugaban ma'aikatan fadarsa, ya sake maida shi kwamishinan kasafi da yake kai tun 2015.

Kara karanta wannan

Takarar Shugaban kasa: Fito-na-fito da Tinubu, da kalubale 4 da suke jiran Osinbajo a 2023

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng