Yadda yunkurin kakaba Ministan Buhari ya yi takarar Gwamna yake barka APC a Kebbi

Yadda yunkurin kakaba Ministan Buhari ya yi takarar Gwamna yake barka APC a Kebbi

  • Zargin kokarin kakaba Abubakar Malami a matsayin ‘dan takarar gwamna ya jawo matsala a APC a Kebbi
  • An samu rabuwar kai sosai tsakanin ‘ya ‘yan jam’iyyar APC a reshen jihar Kebbi saboda wannan shiri
  • Bangaren Sanata Aleiro da Yahaya Abdullahi su na rigima da Gwamna Bagudu mai goyon bayan Malami

Kebbi – Wani hasashe da Premium Times tayi ya nuna an samu wasu a karkashin jagorancin Muhammad Adamu Aliero su na yakar APC a jihar Kebbi.

Lamarin ya rincabe har ta kai Sanatan Kebbi ta tsakiya, Muhammad Adamu Aliero da Sanatan Arewa, Yahaya Abdullahi sun bangarewa jam’iyyar APC.

Sanata Adamu Aliero da Yahaya sun yi yunkurin bude ofishinsu a wani ginin Bello Bagudu, wanda shi kuma yaya ne a wajen gwamna Atiku Bagudu.

Kara karanta wannan

Baki ya ke yanka wuya: An bukaci Tinubu ya bada hakurin abubuwan da ya fada tun 1997

Alamu sun nuna cewa irinsu Sanata Adamu Aliero su na yakar gwamna a kan kokarin da yake yi na damkawa Ministan shari’a tikitin APC a zabe mai zuwa.

Mai magana da yawun bakin ‘yan tawaren, Sani Dododo ya bayyana cewa bangaren jam’iyyar APC da ke tare da gwamnati ta nuna masu son kai da wariya.

Asalin kakakin jam’iyyar APC na reshen jihar Kebbi, Isah Assalafiy ya musanya wannan zargin, ya bayyana abin da ya sa APC ta raba wasu da mukamansu.

Ministan Buhari
Abubakar Malami da Gwamna Bagudu Hoto: kebbistate.gov.ng
Asali: UGC

Mutanen Gwandu kadai ne a Kebbi?

Adamu Aliero wanda ya yi mulki daga 1999 zuwa 2007 ba su goyon bayan Bagudu ya mika mulki ga Malami, su kuma su na goyon bayan Sanata Abdullahi a 2023.

Bagudu da Malami sun fito ne daga yankin Gwandu don haka ake ganin bai kamata a zaben 2023 wani mutumin Birnin Kebbi ya sake darewa kujerar gwamna ba.

Kara karanta wannan

Duk da ya jarraba sa’a sau 3 babu nasara, Sanatan APC zai sake neman Shugaban kasa

Daga 1999 zuwa yanzu, mutanen Kebbi ta tsakiya sun yi gwamna sau biyu. Yankin Arewa sun yi gwamna sau daya, har yanzu kudancin jihar ba ta fitar da gwamna ba.

Gwamna da Minista sun yi gum

Har yanzu gwamna Bagudu bai nuna yana goyon bayan Abubakar Malami ba, shi ma Ministan bai taba fitowa ya fadawa Duniya cewa yana neman gwamna ba.

Rahoton ya ce alamu sun nuna ana kokarin ba Malami takara a APC, a dalilin haka aka fatattaki Muhammad Kangiwa daga kujerar da yake kai na shugaba a jiha.

A wannan rikicin ne aka sauke shugabannin majalisar dokokin Kebbi, aka nada wasu dabam. Ana zargin wadanda aka zaba za su yi abin da gwamna yake so.

Rikicin siyasar PDP

A makon nan ne shugaban Vanguard for Justice, Emmanuel Ndukaya ja-kunnen PDP, ya ce idan aka hana yankin Kudu kawo shugaban kasa, PDP za ta zama tarihi

Kara karanta wannan

Tseren shugabancin APC ya koma tsakanin Sanatoci 2, da tsohon Ministan Buhari

Emmanuel Nduka ya ce idan ana neman adalci da zaman lafiya, dole Arewa su hakura da mulki da zarar Muhammadu Buhari ya gama wa’adinsa na shekaru takwas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel