Buni ya musanta rade-radin fitar da shiyar da APC za ta ba takarar shugaban kasa

Buni ya musanta rade-radin fitar da shiyar da APC za ta ba takarar shugaban kasa

  • Shugaban kwamitin rikon kwarya, Buni har ya ce yanzu jam’iyyar APC ba ta yanke shawarar yankin da za ta tsayar da dan takarar ta ba da ofisoshin kwamitin rikon kwaryar ta ba
  • A ranar Talata da dare, jerin sunaye ya bayyana a kafafen sada zumunta dauke da bayani a kan yadda jam’iyyar ta tsayar da dan takarar shugaban kasa daga kudu
  • Sannan a bayanin an ga yadda NWC ta mika mukami daban-daban daga yankunan da ke kasar nan, don haka hadimin Buni, Mamman Mohammed ya saki takardar wacce ta musanta hakan

Har yanzu jam’iyyar APC ba ta tsayar dayankin dan takarar ta na shugaban kasa ba ko kuma mukamai daban-daban na kwamitin rikon kwarya, NWC, cewar shugaban NWC, Mai Mala Buni, kamar yadda TheCable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Dawo-dawo: Hotunan fostocin Jonathan sun karade titunan Abuja da Legas

A ranar Talata da dare, aka samu jerin sunaye wadanda suka dinga yawo a kafafen sada zumunta wanda ya nuna yadda jam’iyyar ta tsayar da yankin dan takarar shugaban kasa a yankin kudu da kuma wasu masu matsayi a jam’iyyar na NWC daga yankuna daban-daban.

Buni ya musanta rade-radin fitar da shiyar da APC za ta ba takarar shugaban kasa
Buni ya musanta rade-radin fitar da shiyar da APC za ta ba takarar shugaban kasa. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

A wata takarda ta ranar Laraba, Mamman Mohammed, hadimin Buni ya yanko inda Buni ya ke cewa jerin sunayen na bogi ne.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mohammed ya ce gwamnan jihar Yobe ya bukaci kada kowa ya yarda da jerin inda yace wani ne kawai ya zauna ya shirya, TheCable ta ruwaito.

“Mai girma Mai Mala ya musanta wannan jerin sunayen na bogi inda yace karya ne, ba ya da wani tushe balle makama kuma ba ya da wata alaka da shi,” a cewar sa.
“Shugaban kwamitin rikon kwaryar ya ce jam’iyyar ba ta riga ta dauki wani mataki ba a ko wanne mukami.

Kara karanta wannan

2023: Daga ƙarshe, Yahaya Bello ya sanar cewa ya shiga jerin masu son gadon kujerar Buhari

“Wani ne kawai ya zauna ya kago matsayi daban-daban ya jera sunaye. Don haka ina bukatar kowa kada ya yarda don ba gaskiya bane.
“Gwamnan ya bukaci ‘yan jaridu da su dinga tabbatar da labari musamman dangane da jam’iyyar kafin su yada shi.”

Mukarraban Buhari su na jiran matsayarsa a kan takarar Osinbajo, Tinubu a zaben 2023

A wani labari, Na-kusa da Mai girma shugaba Muhammadu Buhari su na jiran ya bayyana ‘dan takarar da yake so a cikin masu harin kujerar shi a zabe mai zuwa.

Punch ta fitar da rahoto cewa hadimai, ministoci da mukarraban shugaban kasar sun gagara marawa kowa a cikin masu neman shugaban kasa baya.

Wadannan mutane su na jiran shugaban kasa ya nuna inda ya karkata domin su san inda suka dosa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel