Dawo-dawo: Hotunan fostocin Jonathan sun karade titunan Abuja da Legas

Dawo-dawo: Hotunan fostocin Jonathan sun karade titunan Abuja da Legas

  • Fostocin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan su na ta yawo a wasu sassan na jihar Legas da Abuja
  • Duk da dai har yanzu akwai ‘yan takarar da suke son tsayawa takara a jam’iyyar APC amma zargin shi zai tsaya
  • Hakan ya janyo fargaba tsakanin ‘yan takarar wacce ta ke da mutanen da ke son tsayawa takara daga kudu

Abuja, Legas - Fostocin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan suna ta yawo a wasu sassa na jihar Legas da Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

Kamar yadda bayanai suka samu dangane da fastocin wadanda aka rubuta “Please Run, Nigerians Are Calling Again”, ka tsaya takara, ‘yan Najeriya suna kara kira”, wata kungiyar Greater Nigeria Ambassadors (GRENA), ne suka shirya fastocin.
Dawo-dawo: Hotunan fostocin Jonathan sun karade titunan Abuja da Legas
Dawo-dawo: Hotunan fostocin Jonathan sun karade titunan Abuja da Legas. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Duk da dai Jonathan bai riga ya bayyana burin sa na tsayawa takarar ba har yanzu, akwai rahotannin da aka samu daga wasu bangare na fadar shugaban kasa da kuma wasu gwamnoni na jam’iyyar APC da suke yakin neman tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2023.

Kara karanta wannan

Gargadin wasu ga PDP: Kada ku ba 'yan shekara 70 tikitin takarar shugaban kasa a 2023

Hakan ya janyo cakudewa a cikin jam’iyyar wacce ta ke da wasu masu fatan tsayawa takara daga kudu, inda ake tunanin daga wanne yanki za ta tsayar da dan takarar ta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A shekarar da ta gabata, jam’iyyar PDP ta zargi APC da bin Jonathan amma APC ta mayar da martani inda tace zai iya shiga jerin masu neman tsayawa takarar.

Jonathan ya dade ba ya zuwa duk wani taro na jam’iyyar PDP da za a yi. Bai je gangamin taron da aka yi na jam’iyyar ba a shekarar da ta gabata, Daily Trust ta ruwaito.

A jihar Legas, an ga fostocin sa a manyan titina kamar Ijaiye, Ogba, Oba, Akran Avenue, karkashin gadar Ikeja da kuma duka hanyoyin titin da filin jirgin Murtala Muhammad a Ikeja.

A Abuja kuwa an ga fstocinsa a AYA, Asokoro da gadar Finance wuraren sakateriyar gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

Damfarar N299.86m: Kotu na neman wani tsohon dan takarar gwamnan Zamfara

An maye gurbin marigayi Umaru Musa Yar’Adua bayan rasuwar Yar’Adua a 2010 ya ci gaba da mulki ya kuma lashe zabe a shekarar 2011 bayan ya tsaya takara.

Sai dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kayar da shi a shekarar 2015 inda Jonathan ya zama shugaban kasa na farko da ya fadi zabe ya na kan mulki.

Shugaba Buhari ya yi ganawar sirri da Goodluck Jonathan

A wani labari na daban, jaridar Daily Trust ta ce, shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba 6 ga watan Oktoba ya yi wata ganawar sirri da tsohon shugaban kasa, Dakta Goodluck Jonathan, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Legit.ng ta tattaro cewa ba a san dalilin ziyarar ba saboda Jonathan bai yi magana da manema labarai ba bayan taron.

Sai dai kuma, an lura cewa tsohon shugaban, a matsayinsa na wakilin ECOWAS na musamman a Mali, yana ta yin taro akai-akai tare da Shugaba Buhari kan kasar ta Yammacin Afirka da ke fama da rikici.

Kara karanta wannan

2023: Zan iya shugabancin Najeriya amma dai ban matsu ba, Orji Kalu

Asali: Legit.ng

Online view pixel