Babban ɗan kasuwa a Arewa ya sanar da shugaba Buhari kudirinsa na takarar shugaban ƙasa a 2023

Babban ɗan kasuwa a Arewa ya sanar da shugaba Buhari kudirinsa na takarar shugaban ƙasa a 2023

  • Wani ɗan kasuwa daga yankin Arewa, Moses Ayom, ya rubuta wa shugaba Buhari, wasika domin sanar da shi kudirin takara a 2023
  • Ayom, ɗan asalin jihar Benuwai, ya shaida wa shugaba Buhari a wasikar cewa yana fatan maye gurbinsa ne domin ɗora wa daga inda zai tsaya
  • Wannan na zuwa ne bayan jagoran APC, Bola Tinubu, da gwamna Dave Umahi, sun sanar da shugaban kudurinsu

Benue - Ɗan takarar shugaban ƙasa karkashin APC, Moses Ayom, ya rubuta wasika zuwa ga shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, domin sanar da shi kudirinsa na takara a 2023.

Leadership ta rahoto cewa Ayom, a wasikar mai taken, "Kudirin shiga tseren tikitin shugaban ƙasa a 2023," kuma mai ɗauke da kwanan watan 13 ga watan Janairu, ya bayyana manufofinsa ga ƙasa idan ya cimma burinsa.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga: Abinda Gwamna Masari ya faɗa wa Bola Tinubu kan kawo karshen rikici a jihar Katsina

Moses Ayom
Shahararren ɗan kasuwa ya sanar da shugaba Buhari kudirinsa na takarar shugaban ƙasa a 2023 Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Shahararren ɗan kasuwan, ɗan asalin jihar Benuwai, shi ne ɗan takara na farko da ya bayyana kudirinsa a APC daga yankin arewa ta tsakiya.

Wani sashin wasikar yace:

"Tare da tsantsar girmamawa, Ni Moses Chiahemba Ayom, mamban jam'iyyar APC, ina mai sanar maka da manufa ta na neman ofishin shugaban ƙasa a zaben 2023, karkashin jam'iyyar mu."

Meyasa Ayom yake son zama magajin Buhari?

Mista Ayom, ya bayyana cewa ya ɗauki matakin neman kujera lamba ɗaya a Najeriya ne domin ɗorawa daga inda shugaba Buhari zai tsaya.

"Na ɗauki wannan matakin ne saboda kyakkyawan jagorancin ka da kudurorin ka na kawo cigaba a ƙasa Najeriya."
"Yadda kake tafiyar da tattalin arzikin ƙasa da kuma manyan ayyukan raya ƙasa da muka shaida da idanun mu, suna bukatar wanda zai jajirce ya ɗora daga nan."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun yi awon gaba a da daliban jami'ar Tarayya a Nasarawa

Sauran yan takaran da suka sanar da Buhari a APC

Idan baku mance ba, mun kawo muku rahoton cewa jagoran APC na ƙasa, Bola Tinubu, ya sanar da Buhari kudirinsa na takara a 2023.

Kazalika, bayan awanni 24 da haka, gwamnan jihar Ebonyi. Dave Umahi, yaje fadar shugaban ƙasan, ya gaya wa Buhari na shi kudurin na shiga tseren tikiti.

Bola Tinubu, ya fito ne daga yankin kudu maso yammacin Najeriya, yayin da gwamna Umahi, ya fito daga kudu maso gabas.

A wani labarin na daban kuma Jam'iyyar APC ta bayyana gwamnan da zata goyi baya ya gaji shugaba Buhari a 2023

Jam'iyyar APC ta nuna goyon bayanta 100 bisa 100 kan takarar gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi a zaben 2023.

Shugaban APC reshen jihar Ebonyi, Mista Emegha, yace matukar gwamnansa ya zama shugaban ƙasa, to Najeriya zata yi gogayya da sauran ƙasashe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel