Gwamnonin APC sun shiga ganawa yayin da rikicin kan taron gangamin jam'iyyar ya kazanta

Gwamnonin APC sun shiga ganawa yayin da rikicin kan taron gangamin jam'iyyar ya kazanta

  • Gwamnonin jam'iyyar APC sun shiga ganawa kan rikicin jam'iyyar da ke sake rincabewa kafin gangamin zaben sabbin shugabannin jam'iyyar
  • Gwamnonin da suka hallara sun hada da Zulum na jihar Borno, Matawalle na jihar Zamfara, Abdurrazaq na Kwara da sauransu
  • Ana taron ne a masaukin gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, da ke yankin Asokoro na babban birnin tarayya da ke Abuja

FCT, Abuja - Gwamnoni karkashin jam'iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC) sun shiga taro domin neman matsaya kan gangamin taron jam'iyyar da za a yi.

Ana taron ne a masaukin gwamnan jihar Kebbi da ke yankin Asokoro da ke Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnonin APC sun shiga ganawa yayin da rikicin kan taron gangamin jam'iyyar ya kazanta
Gwamnonin APC sun shiga ganawa yayin da rikicin kan taron gangamin jam'iyyar ya kazanta. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Rikici ya na cin jam'iyyar mai mulki tun bayan da kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar karkashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni ya kasa shirya taron zaben sabbin shugabannin jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Gwamnoni sun tsaida matsaya kan zaben shugabanni da makomar Buni a taron Abuja

A watan Nuwamban 2021, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da manyan shugabannin jam'iyyar a gidan gwamnati da ke Abuja, inda aka amince kan cewa za a yi zaben sabbin shugabannin jam'iyyar a watan Fabrairu, duk da ba a tsayar da rana ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sakataren kwamitin rikon kwarya, Sanata John James Akpanudoedehe a wata takarda da ya fitar a makon da ya gabata, ya ce kwamitin ya na tuntubar masu ruwa da tsaki kafin taron, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnonin APC da suka halarci taron sun hada da; Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni; Babagana Zulum (Borno), Abubakar Badaru (Jigawa), Rotimi Akeredolu (Ondo), Abubakar Bello (Niger), Nasir El-Rufai (Kaduna), Kayode Fayemi (Ekiti), Yahaya Bello (Kogi), Ben Ayade (Cross River), Dapo Abiodun (Ogun).

Sauran sun hada da; Gwamnan jihar Zamfara , Bello Matawalle, David Umahi (Ebonyi), Gboyega Oyetola (Osun), Babajide Sanwolu (Lagos), Hope Uzodimma (Imo), Solomon Lalong (Plateau), Abdullahi Sule (Nasarawa), and Abdulraman Abdulrazaq (Kwara).

Kara karanta wannan

Ina mata fatan alkhairi, amma mafi alkhairin mutum muke bukata a 2023: Gwamnan Oyo ga Tinubu

2023: Rikicin APC na cigaba da jagwalewa, ta kacame tsakanin Bagudu da Aliero

A wani labari na daban, rikici ya na ci gaba da kamari tsakanin gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu da Sanata Adamu Aliero wanda hakan zai janyo rabuwar kawuna a jam’iyyar APC a jihar, Daily Trust ta ruwaito a ranar Lahadi.

Shugabannin jam’iyyar na kasa da jihar sun bayyana wa manema labarai cewa, daga Bagudu har Aliero su na da wanda suke son a tsayar takarar gwamna a jam’iyyar APC.

Rahotanni sun nuna yadda Bagudu wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin arewa ya ke so a daura antoni janar, Abubakar Malami a matsayin dan takara, yayin da Alieru wanda ya yi gwamna har sau biyu a jihar, yake son a tsayar da Yahaya Abdullahi, wanda shugaba ne na majalisar dattawa a dan takarar gwamnan jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel