2023: Rikicin APC na cigaba da jagwalewa, ta kacame tsakanin Bagudu da Aliero

2023: Rikicin APC na cigaba da jagwalewa, ta kacame tsakanin Bagudu da Aliero

  • Rikici ya na ci gaba da barkewa tsakanin gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi da Sanata Adamu Alieru akan wanda zai gaji kujerar gwamnan idan ya sauka
  • Shugabannin jam’iyyar APC sun bayyana yadda ko wanne daga cikin Bagudu har Aliero ya ke da burin kawo wanda zai tsaya takarar gwamna, hakan ya janyo rikicin
  • Rahotanni sun nuna yadda Bagudu yake son Antoni janar, Abubakar Malami ya gaje shi, yayin da Alieru yake son shugaban majalisa, Yahaya Abdullahi ya gaje shi

Kebbi - Rikici ya na ci gaba da kamari tsakanin gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu da Sanata Adamu Aliero wanda hakan zai janyo rabuwar kawuna a jam’iyyar APC a jihar, Daily Trust ta ruwaito a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Dele Momodu: Allah ne ya tanade ni na gaji Buhari a zaben 2023

Shugabannin jam’iyyar na kasa da jihar sun bayyana wa manema labarai cewa, daga Bagudu har Alieru su na da wanda suke son a tsayar takarar gwamna a jam’iyyar APC.

2023: Rikicin APC na cigaba da jagwalewa, ta kacame tsakanin Bagudu da Aliero
2023: Rikicin APC na cigaba da jagwalewa, ta kacame tsakanin Bagudu da Aliero. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Rahotanni sun nuna yadda Bagudu wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin arewa ya ke so a daura antoni janar, Abubakar Malami a matsayin dan takara, yayin da Alieru wanda ya yi gwamna har sau biyu a jihar, yake son a tsayar da Yahaya Abdullahi, wanda shugaba ne na majalisar dattawa a dan takarar gwamnan jihar.

Daga Malami har Abdullahi ba su bayyana ra’ayinsu na tsayawa takarar gwamnan ba amma na kusa da su sun bayyana cewa lokacin da ya dace kawai suke jira.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kudirin Aliero kamar yadda Daily Trust ta ruwaito a ranar Lahadi, ya janyo rabuwar kawuna a jam’iyyar APC reshen jihar Kebbi.

Kara karanta wannan

Hotunan Buhari yayin da ya ziyarci iyalan Marigayi Shonekan don yi masu ta’aziyya

Yayin da gwamna Bagudu, Malami da mabiyansu suka rabe bangare, Sanata Alieru, shugaban majalisa da mabiyansa sun koma gefe guda.

A bangaren Alieru, akwai Bala Sani Kangiwa wanda aka tube a taron jam’iyyar daga shugaba, yayin da gwamnan ya ke da Abubakar Kana Zuru a matsayin shugaba na jam’iyyar. Yanzu haka akwai ofisoshin jam’iyyar na jihar guda biyu a Birnin Kebbi, babban birnin jihar.

Wani dan majalisa ya sanar da manema labarai cewa, Bagudu da Alieru sun janyo rabuwar kawuna a jam’iyyar duk da Alieru ya taka babbar rawa wurin tsayar da Bagudu a takarar gwamnan shekarar 2015, amma tun bayan nan suka bata.

“Ya kamata Aliero ya tsaya haka. Ya na so ya tsayar da shugaban majalisar jihar amma dan takarar gwamnan Malami ne. Hakan ya janyo rabuwar kawuna a jihar Kebbi,” a cewar majiyar wacce ta bukaci a sakaya sunan ta.
Ya kara da cewa, “akwai matsalolin da ka iya barkewa idan har APC a jihar Kebbi ta ki yin adalci. A wancan taron saboda son zuciya aka tube shugaban jam’iyyar sannan aka daura wani. Ba za mu bari hakan ya ci gaba ba."

Kara karanta wannan

Fitaccen dan jarida, Dele Momodu ya ayyana kudurin tsayawa takara a 2023 a PDP

Ba a samu damar tattaunawa da Bagudu ba, amma shugaban jam’iyyar na bangaren su ya ce ba ya da masaniya a kan dayan bangaren jam’iyyar APC a jihar Kebbi.

Rikicin APC a Kano: Lauyan Ganduje ya musanta lallasa su da su Shekarau suka yi a kotu

A wani labari na daban, daya daga cikin lauyoyin da ke kare bangaren APC din jihar Kano ta Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a shari’ar da su ke yi ya ce ba su sha kaye a shari’ar da aka yi a kotun Abuja ba.

Yayin tsokaci dangane da rahotannin da ake yadawa a kan shari’ar, Barista Abdullahi Adamu Fagge ya sanar da Daily Trust cewa mutane sun dinga sauya asalin abinda aka yi a kotu don nuna kamar bangaren Ganduje sun fadi shari’ar ne.

Ya bayyana yadda alkalin kotun, Mai shari'a Hamza Muazu ya ce ba zai ci gaba da sauraron karar ta bangaren Ganduje ba saboda ba shi da hurumin yin hakan, sai dai su daukaka kara zuwa kotun daukaka kara.

Kara karanta wannan

An gano dalilin kus-kus din Gwamnan APC da Tinubu sa'a 48 da ayyana niyyar takara

Asali: Legit.ng

Online view pixel