Matar aure ta tsere da saurayinta ta bar mijinta da suka shafe shekaru 3 tare

Matar aure ta tsere da saurayinta ta bar mijinta da suka shafe shekaru 3 tare

  • Wata kotu mai zama a Kasuwan Nama cikin garin Jos ta raba aure mai shekaru uku da ke tsakanin Adaka Yunana da matarsa Helen bayan ta tsere da wani saurayin ta
  • Alkalan kotun, Ghazali Adam da Hyacinth Dolnanan sun amince da raba auren bisa bukatar Yunana bayan yin iyakar kokarinsu don shirya su amma abin ya ci tura
  • Kamar yadda mijin ya shaida wa kotu, matar ba ta yi masa wani bayani ko kuma ta ba shi wasu hajjojin son rabuwa da shi ba, kawai nemanta ya yi ya rasa

Jihar Plateau - Wata kotu mai zamanta a Kasuwan Nama cikin garin Jos ta datse igiyan auren wasu ma'aurata da suka shafe shekaru uku tare, a ranar Alhamis, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Bayan amsan N10m hannun saurayi, Bazawara tace ta fasa aurensa ana saura kwana 10 aure

An raba auren da ke tsakanin Adaka Yunana da matarsa, Helen, bayan ta tsere ta bi saurayinta.

Matar aure ta tsere da saurayinta ta bar mijinta da suka shafe shekaru 3 tare
Kotu ta raba aure bayan mata ta bar mijinta na aure, ta tsere da saurayinta. Hoto: The Nation
Asali: Twitter

Alkalan kotun, Ghazali Adam da Hyancinth Dolnanan, sun amince da bukatar da Yunana ya turo kotun ta rabuwar auren.

An yi kokarin shirya su amma abin bai yiwu ba

Duk da iyakar kokarin da kotun ta yi na ganin ta daidaita tsakaninsu amma abin ya ci tura, hakan ya sa aka raba auren.

The Nation ta bayyana yadda alkalan su ka bukaci Yunana da Helen su rabe alakar auren da ke tsakaninsu, kowa ya kama gabansa.

Ya ce bata sanar da shi dalilinta na yin hakan ba

Dama tun farko Yunana ne ya kai korafi ga kotun wanda ya bukaci a raba aurensu, kamar yadda ya shaida:

Kara karanta wannan

Yadda magidanci ya kashe matarsa da duka bayan sun samu sabani a Nasarawa

“Mata ta ta tsere don ta ci gaba da zama da saurayinta a 2019, shekarar da na aure ta.
“Ko kira na don ta sanar da ni dalilin da ya sa ta yi hakan ba ta yi ba, haka kuma ko da na kira ta.”

Ba zan iya ba: Jarabar mijina ta yi yawa, yana so ya kashe ni da saduwa, Matar aure ga kotu

A wani labarin, wata matar aure mai 'ya'ya uku, Olamide Lawal, a ranar Juma'a ta roki kotun Kwastamare da ke zamansa a Mapo, Ibadan, ya raba aure tsakaninta da mijinta, Saheed Lawal, saboda yana jarabar ta da yawan saduwa, rahoton Premium Times.

A karar da ta shigar, Olamide wacce ke zaune a Ibadan ta kuma yi ikirarin cewa mijinta ya saba shan giya ya yi tatil yana maye, The Nation ta ruwaito.

Ta ce:

"Mun shafe shekaru 14 muna zaman aure da Lawal. Tantirin mashayin giya ne kuma ba shi da tausayi ko kadan a zuciyarsa.

Kara karanta wannan

Angon Instagram: Yadda budurwa ta cire kunya tayi abin da ya dace, ta yi wuf da matashi

"Abin da ya mayar da hankali a kai shine shan giya, duka na da kuma tilasta min kwanciyar aure da shi. Baya kulawa da yaran mu.
"Ba zan iya cigaba da zama tare da shi ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel