Shugaban kwamitin yakin neman zabe ya gagara fadin silar dukiya da ainihin shekarun Tinubu

Shugaban kwamitin yakin neman zabe ya gagara fadin silar dukiya da ainihin shekarun Tinubu

  • Hon. Abdulmumin Jibrin shi ne Shugaban yakin neman zabe na Tinubu Support Management Council
  • Tinubu Support Management Council na kokarin ganin Jigon APC, Bola Tinubu ya zama shugaban kasa
  • Da aka yi wa Hon. Jibrin wasu tambayoyi a game da Tinubu, bai iya bada wata gamsashiyyar amsa ba

Abuja - A wata hira da aka yi da Darekta Janar na tafiyar Tinubu Support Management Council, Hon. Abdulmumin Jibrin, an tabo batun dukiyar Bola Tinubu.

Jaridar Premium Times ta Honarabul Abdulmumin Jibrin ya yi ta shiga nan-ya fita can a lokacin da aka bijiro masa da tambayar dukiya da shekarun mai gidansa.

Ana zargin Bola Ahmed Tinubu ya tara makudan dukiyar da akwai alamar tambaya a kan ta. Haka zalika akwai shakku game da ikirarin cewa shekararsa 69.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Na shirya yin gaba da gaba da Tinubu a zaben fidda gwanin APC – Shahararren sanata

Da ya zanta da gidan talabijin na Arise, an nemi gaskiyar magana a kan silar arziki da kuma shekarun Tinubu, amma Abdulmumin Jibrin ya yi ta kame-kame.

Tambayar da ba ta da amsa

Tambayar da aka yi wa Hon. Abdulmumin Jibrin shine ya aka yi aka ga motar kudi a cikin gidan Tinubu ranar zabe, kuma shin menene asalin shekarunsa a Duniya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tsohon ‘dan majalisar ya ce abin da ya dace a tambaya shi ne kwarewa da cancantar Tinubu, sannan ya gaza wanke gwaninsa daga zargin rashin gaskiya a hirar.

Tinubu
Tinubu da Buhari a Aso Rock Hoto: Facebook
Asali: Facebook

Martanin da Jibrin ya bada

“Na amsa wannan tambayar a baya. Ina ganin a matakin da mu ke yanzu, abin da ya kamata a maida hankali a kai shi ne abin da ‘dan takarar nan ya yi a baya.”
“Idan ku ka cigaba da yin wannan tambaya kullum, za ku cigaba da samun amsa iri daya. Duk tarkace ne da mutane ke fada a yanar gizo, babu wani abin kirki.”

Kara karanta wannan

Addini, rashin lafiya, da matsaloli 5 da Tinubu zai fuskanta a neman Shugaban Najeriya

“Idan aka fara yakin neman zabe, za mu fitowa mutanen Najeriya da alkaluma na gaskiya.”

- Hon. Abdulmumin Jibrin.

Mulki ba a shekaru ba ne

Da ‘dan jarida ya sake nanata wannan tambaya, sai ‘dan siyasar ya bukaci ya yi hakuri da amsar da ya bada, ya ce idan bai gamsu ba, sai ya shiga wata gabar dabam.

Jibrin yana ganin cewa babu ruwan sha’anin mulki da shekarun shugaba inda ya ce za iya samun matashi mai ilmi ya gaza, ko a samu mai shekara 70 da ya iya mulki.

GEJ: Ka yi hattara da APC - Sule

A makon jiya ne aka ji Sule Lamido ya fadawa Goodluck Jonathan ya yi hattara da shigo-shigo babu zurfin ‘Yan APC kan zakin-bakin ba shi takarar shugaban kasa.

Hakan na zuwa ne a lokacin da ake ta rade-radin cewa Goodluck Jonathan zai shiga jam'iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel