Tsohon Gwamna ya fadawa Jonathan abin da zai faru da shi idan ya koma APC, ya yi takara

Tsohon Gwamna ya fadawa Jonathan abin da zai faru da shi idan ya koma APC, ya yi takara

  • Sule Lamido ya yi magana a kan yiwuwar sake neman takara da komawar Goodluck Jonathan APC
  • Tsohon gwamnan na jihar Jigawa yace shekaru biyu kacal suke ragewa Goodluck Jonathan a dokar kasa
  • Jigon na PDP yana ganin Dr. Jonathan zai bata sunan da ya tsira da shi idan ya sake neman takara

Jigawa - Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya zanta da jaridar nan ta The Sun, inda kamar yadda ya saba, ya tabo batutuwan siyasar APC da PDP.

A wannan hira da aka yi da jigon na PDP, ya bayyana hikimar dauko Dr. Iyorchu Ayu da aka yi a matsayin sabon shugaban jam’iyya da kuma shirin zaben 2023.

Alhaji Sule Lamido ya gargadi tsohon shugaban Najeriya, Dr. Goodluck Jonathan a kan tayin da wasu ‘ya ‘yan APC suke yi masa na shiga cikin jam’iyyar ta su.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Ministan Buhari ya bayyana yarjejeniyar da aka yi tun wajen kafa APC

Da farko Sule yana ganin tun da Jonathan ya yi shekaru shida a mulki, dokar kasa ba ta ba shi dama ya kara wani wa’adi ba domin zai haura shekaru takwas.

Saura masa shekaru biyu rak

“Idan ana maganar tsarin mulki, zai zo ne ya karasa ragowar shekaru biyu, sai ya sauka daga kujerar shugaban kasa? Ta ya ya za ayi wannan?”
“Shekara takwas ake yi a mulki, shi ya yi shekaru shida kuma ana cewa ya dawo ya karasa wa’adinsa. Shekara biyu zai yi ko hudu kenan?”
Ekiti 2014
Jonathan wajen kamfe a Ekiti Hoto: www.thecable.ng
Asali: UGC

“Yanzu kuma sun dawo su na zuga shi ya shiga APC. Ya tsaya ya yi tunani, ba su ne mutanen da suka ci masa mutunci ba? Yau sun lallabo wurinsa."
“Idan ya na so ya je, ga fili ga mai doki. Bai san mecece APC ba. Bai san su ba, inda matsalar ta ke kenan. Ana masa kallon mutunci, ya tsira da wannan.”

Kara karanta wannan

Karya ake yi mani na cewa ina shirin barin PDP, in sake komawa APC inji Rabiu Kwankwaso

-Sule Lamido

Idan ma ya na sha’awar zama shugaban kasa, Sule yace zai fi kyau Jonathan ya nemi takara a PDP, amma dole sai ya shiga zaben fitar da gwani yadda aka yi a 2011.

Sule Lamido ya bada labarin ganawar da ya yi da Jonathan bayan PDP ta sha kasa a takarar shugaban kasa a zaben 2015, ya ba shi shawarar ya rike Ubangijinsa.

‘Dan siyasar yace ya fadawa Jonathan a wancan lokacin cewa wasu za su iya neman a haukata sa. Yanzu kuma yana neman biyewa APC domin ya bata sunansa.

Dawowar GEJ a 2023

Dazu kun ji cewa har yanzu manyan jagororin APC ba su gama yarda a shigo da Goodluck Jonathan, a ba shi takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa na 2023 ba.

Ganin yadda ake wulakanta sa a PDP, wasu Gwamnonin Arewa na APC suka dage sai sun shigo da Jonathan cikin jam'iyya, amma shirin na su bai samu karbuwa ba.

Kara karanta wannan

2023: Ku samu katikan zaben domin zaben shugabanni nagari, Sanusi

Asali: Legit.ng

Online view pixel