Tun kafin a shirya zaben fitar da gwani, Gwamnan APC ya fadi wanda zai damkawa mulki

Tun kafin a shirya zaben fitar da gwani, Gwamnan APC ya fadi wanda zai damkawa mulki

  • Ben Ayade yace 2023 lokaci ne da mutanen yankin Kudancin jihar Kuros Riba za su fito da Gwamna
  • Gwamna Ayade ya tabbatarwa ‘Yan APC cewa zai cika alkawarin ganin ‘Dan Kudu ne ya gaje shi
  • Tun bayan Donald Duke a 2003, ba a samu Gwamna a Kuros Riba daga yankin kudancin jihar ba

Cross River - Mai girma gwamnan jihar Kuros Riba, Ben Ayade ya ce ba zai mika mulki ga duk wanda ba daga yankin kudancin Kuros Riba ya fito ba.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Dr. Ben Ayade yana wannan magana a karshen makon da ya gabata.

Da yake zantawa da shugabanni da masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC a garin Kalaba, Gwamna Ben Ayade ya sake tabbatar da matsayar da yake kanta.

Ana ta rade-radin cewa Ayade ya lashe amansa, amma a wannan zama ya jaddada cewa yana nan kan cewa sai mutumin kudancin jihar ne zai gaje shi.

“Ban canza shawara ba. Ni na tursasawa kai na cewa sai mulki ya koma yankin kudancin jihar a zaben 2023.”
“Ko ba a fada ba, abin da ya kamata ayi kenan. Kowane yanki zai fito da gwamna a haka.”

- Dr. Ben Ayade

Gwamnan K/Riba
Gwamna Ayade Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Zan cika alkawarin da na yi - Ayade

Mai girma gwamnan yace zai cika wannan alkawari da ya daukarwa kansa na ganin mutanen kudancin jihar Kuros Riba sun samu damar yin gwamna.

Hukumar dillacin labarai na kasa ta rahoto Ayade yana cewa akwai ‘yan siyasa daga yankin kudancin jihar Kuros Riba da suka cancanci su yi gwamnan.

“Da nake yakin neman tazarce, na je yankin kudu na kuma roki su mara mani baya in zarce a mulki, na ce idan na ci zabe, zan goyi bayan su gaje ni.”
“Abin da ya kamata ayi kenan, gwamna da zai zo,, ya fito daga mazabun da ke kudancin jihar.”

- Dr. Ben Ayade

Da yake jawabi a gidan gwamnati da ke Kalaba, Ayade yace akwai bukatar a rika yin adalci a siyasa, ba a rika maida hankali kurum a kan yawan kuri’u ba.

Za mu kawo gyara - Kungiyar

A makon nan ne aka ji cewa kungiyar Patriotic Volunteers Association ta bayyana a Kano da nufin tsabtace tsarin siyasar da ake tafiya a kai a zaben 2023.

Patriotic Volunteers Association ta na kokarin ganin an daina siyasar kudi, an bi nagarta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel