Ba a gama shawo kan rikicin Shekarau v Ganduje ba, APC ta sake bangarewa a jihar Kano

Ba a gama shawo kan rikicin Shekarau v Ganduje ba, APC ta sake bangarewa a jihar Kano

  • Wata kungiya mai suna Patriotic Volunteers Association ta bayyana a karkashin APC a jihar Kano
  • Tsohon kwamishinan Kano, Ibrahim Dan Azumi Gwarzo ne shugaban Patriotic Volunteers Association
  • Alhaji Ibrahim Dan Azumi Gwarzo yace za su yi kokarin yakar siyasar kudi, a zabi masu nagarta

Kano – A karshen makon jiya ne wata sabuwar kungiya mai suna Patriotic Volunteers Association ta bayyana a jam’iyyar APC ta reshen jihar Kano.

Daily Trust ta fitar da rahoto cewa an kafa wannan kungiya ne a ranar Lahadi, 9 ga watan Junairu, 2022 domin a kawo gyara a harkar siyasar kasar nan.

Burin Patriotic Volunteers Association shi ne tsaida ‘yan takara masu nagarta a zaben 2023 ta yadda wadanda suka cancanta za su samu kujeru da mukamai.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Diyar sarki ta rasu kwanaki kadan bayan rasuwar mahaifinta

Da yake magana da manema labarai a makon da ya gabata, shugaban kungiyar, Ibrahim 'Dan Azumi Gwarzo ya bayyyana cewa akwai bukatar kawo gyara.

Alhaji Ibrahim 'Dan Azumi Gwarzo wanda ya taba rike Kwamishina a gwamnatin jihar Kano yace su na so ne a rika tafiya a kan turbar damukaradiyya na asali.

Gwamnan jihar Kano
Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Mun saki layi - Ibrahim 'Dan Azumi Gwarzo

Jaridar ta rahoto 'Dan Azumi Gwarzo yana cewa Patriotic Volunteers Association ta na sha’awar ganin ana siyasa a Najeriya kamar yadda ake yi a kasashen waje.

Shugaban wannan tafiya yace su ‘ya ‘yan APC ne kuma su na aiki ne a karkashin jam’iyyar.

Rahoton Vanguard ya bayyana cewa Patriotic Volunteers Association ta na so a daina siyasar kudi, a rika tsaida shugabanni bisa cancanta da nagartarsu.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Mummunar gobara ta yi kaca-kaca da wani gida, uwa da jaririnta sun kone a Kano

Jawabin shugaban Patriotic Volunteers Association

“Najeriya ta dauko aron damukaradiyya daga kasar Amurka, amma abin takaicin shi ne ba mu dauko sauran abubuwa masu kyau da ke tattare da tsarin ba.”
“A Amurka babu wanda yake yin takara saboda yana da kudin da zai raba, ana duba cancanta ne da aikin mutum. Ba don haka ba, da Obama ba zai yi mulki ba.”
“Abin takaici mu a nan ana amfani da siyasar kudi, ba zai yiwu mu cigaba da yin haka ba. Mu na da kishi, don haka dole ayi gyara, ko a cigaba da tafiya a baibai.”

- 'Dan Azumi Gwarzo

Kan gwamnonin APC ya rabu

Kun ji cewa a karshen bara ne wasu shugabannin jam’iyyar suka yi zama da Muhammadu Buhari inda aka amince ayi zaben shugabanni na kasa a Fubrairu.

A halin yanzu wasu daga cikin ‘ya ‘yan APC sun huro wuta, su na so kwamitin rikon kwaryan da Mai Mala Buni yake jagoranta ya daga lokacin shirya zaben.

Kara karanta wannan

Da an ji kunya, bai dace mu ba Jonathan takarar shugaban kasa ba - Tsohon Hadimin Buhari

Asali: Legit.ng

Online view pixel